✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan ISWAP sun yi artabu da mafarauta a Borno

Mayakan ISWAP din suna shiga garin suka hau harbi kan mai uwa da wabi.

An yi musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar ISWAP da mafarauta bayan kungiyar ta kai farmaki a wani kauye da ke Kudancin Jihar Borno, kamar yadda majiyar CJTF ta bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan ISWAP sun hari kauyen Shallangba da ke yankin Debiro ne a Karamar Hukumar Hawul, a kan babura inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su tsere zuwa daji.

Majiyar ta bayyana cewar har zuwa yanzu wasu daga cikin mayakan na cikin kauyen, inda suke ta dauki ba dadi da mafarautan kauyen.

A ranar Lahadi ne Boko Haram ta farmaki yankin na Debiro, wanda ke da iyaka da kananan hukumomin Biu da Hawul  a Jihar Borno.