Ana zargin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kashe akalla mutum 27 a wani mummunan hari da ta kai kauyen Tormour a yankin Diffa na jamhuriyyar Nijar a Yammacin ranar Asabar.
Harin da mayakan Boko Haram suka kai Kudu maso Gabashin Nijar a daren Lahadi sun kone gidaje, motoci da kuma wata babbar kasuwa kamar yadda hukumomi da mashaida suka tabbatar.
- Yadda aka daura auren matashin Kano da Ba’amurikiya
- Cikin ‘’yan sa’o’i’ za mu ceto daliban Katsina —Ministan Tsaro
- ’Yan Boko Haram sun kai hari wani gari a Borno, sun yi kiran Sallah
Da dama daga cikin wadanda harin ya ritsa da su sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka na harsashin bindiga, baya ga wadanda suka kone kurmus sakamakon wuta da maharan suka cinna a gidajensu.
Bayanan mahukunta ya nuna cewa kimanin gidaje 800 zuwa 1,000 aka kone a harin da mayakan Boko Haram kimanin 70 suka kai kauyen na Tourmour a kasa bayan sun ketaro ta tafkin Chadi.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, maharan sun kashe mutane da dama bayan bude musu wuta, inda dirarsu ke da wuya suka fara da gidan mai gari amma ya tsallake rijiya da baya.
A tsawon awanni uku da maharan suka shafe suna cin karensu babu babbaka, sun kone kaso 60 cikin 100 na kauyen kamar yadda mahukunta suka tabbatar.