✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun kai hari Dapchi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayakan Boko haram ne sun kai hari Dapchi, hedkwatar karamar hukumar Bursari da ke jihar Yobe, da maraicen Litinin.…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayakan Boko haram ne sun kai hari Dapchi, hedkwatar karamar hukumar Bursari da ke jihar Yobe, da maraicen Litinin.

Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar Daily Trust cewa maharan sun banka wa gidan hakimin Dapchi wuta, sun kuma balla shaguna sannan suka yi awon gaba da kayan abinci da wasu abubuwan.

Wani mazaunin yankin da ya yi magana da wakilin Daily Trust ta waya ya ce da kusan karfe 6.00 na yamma aka kai harin a daidai lokacin da mazauna garin, wadanda galibinsu Musulmi ne, ke shirye-shiryen shan ruw.

“Masu ta da kayar bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi, amma daga bisani harbe-harben suka lafa”, inji shi.

“Amma a yanzu da nake magana da kai muna jin harbe-harbe ba kakkautawa daga bangarori daban-daban na garin; na yi amanna sojoji ne suke dauki ba dadi da maharan”.

Ya kuma ce ba zai yiwu a tantance wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata ba, saboda har zuwa lokacin da yake magana ba a kawo karshen harin ba.

Ranar 19 ga watan Fabrairun 2018 ne dai mayakan Boko Haram suka sace ’yan mata 110 daga Kwalejin Kimiyya ta ’Yanmata da ke Dapchi.

A watan Maris din 2018 aka saki dukkan ’yanmatan, ban da Leah Sharibu, wacce ita kadai ce Kirista a cikinsu.

%d bloggers like this: