✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawakiya Rihanna ta sake samun juna-biyu da Rocky

Kafafen sada zumunta sun dumama da bayyanar juna-biyun Rihanna ba zato ba tsammani, lokacin da take gudanar da wasan ‘Super Bowl’ na bana a Amurka.…

Kafafen sada zumunta sun dumama da bayyanar juna-biyun Rihanna ba zato ba tsammani, lokacin da take gudanar da wasan ‘Super Bowl’ na bana a Amurka.

Tun bayan furta cewa akwai yiwuwar ta gabatar da wani bako na musamman lokacin wasan kamar yadda yake a al’adar wasan a wata hira da ta gudanar makon da ya gabata, masoyanta suka shiga hasashen wane ne.

Sai dai duk canke-canken cewa daya daga cikin fitattun mawaka Jay-Z ko Drake ko Eminem za ta gabatar, sai ga shi ta bayyana ashe a kan juna-biyun da take dauke da shi ne.

Mawakiyar sanye da jajayen kaya, ta cashe da wakokinta da dama da suka yi shura a duniya irin su Umbrella da Diamond da Better Have My Money da sauransu.