✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawaƙin siyasa Garba Gashuwa ya rasu

Gashuwa ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 11.

Allah Ya yi wa shahararren mawakin siyasar nan, Alhaji Garba Gashuwa rasuwa.

Ƴar marigayin, Maryam Garba Gashuwa ce sanar da rasuwarsa.

Maryam ta shaida wa Aminiya cewa mahaifin nasu ya rasu yau Lahadi da asuba a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano. bayan ya sha fama da jinya.

A cewarta, mahaifin nata ya haura shekara 70 kafin rasuwarsa.

Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 11 da kuma jikoki da dama.

Gashuwa ya shahara wajen yi wa masu mulki wakoki tun lokacin mulkin soja har zuwa na farar hula.

Mafi shahara a wakokinsa ita ce wacce ya yi wa Shugaban Kasa na mulkin soja a wancan lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Sannan ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari waka da kuma jam’iyyarsa ta ANPP lokacin yana yaƙin neman zaɓe.