Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce wadanda suka kai hari Shelkwatar ‘yan sanda a Jihar Imo matsorata ne.
Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya za ta wadatar da jami’an tsaro da dukkan kayan aikin da suka dace don yaki da bata gari a fadin kasar.
- Direban Shugaba Buhari ya riga mu gidan gaskiya
- Yau za a ci gaba da gasar cin kofin zakarun Turai
- Daliban Kaduna: Har yanzu iyayen daliban ba su gana da su ba
- Cutar Murar Tsuntsaye ta barke a jihohi 7 na Najeriya- NCDC
Mataimakin shugaban kasar, ya yi wannan jawabi ne a birnin Owerri na jihar Imo, a ranar Talata, yayin da yake ganewa idonsa irin barnar da aka yi wa shelkwatar ‘yan sandan jihar.
Kazalika, ya ce jami’an tsaro za su kamo dukkanin wadanda ke da hannu harin domin su fuskancin fushin shari’a.
Mataimakin shugaban kasar, ya yi zagayen ganewa idonsa barnar da aka yi tare da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola da kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne wasu mahara dauke da bindigogi da ababen fashewa suka fasa babban gidan yari da shelkwatar ’yan sanda a babban birnin Owerri inda suka saki daruruwan wadanda ke cin sarka.