✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsinkewar kafar sadarwa

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan karon in sha Allah za mu rufe bayanin…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan karon in sha Allah za mu rufe bayanin kan yaren kauna na farko da kuma tattauna matsalar toshewar hanyar sadarwar ma’aurata, wanda hakan na matukar takura ma’aurata, musamman wadanda kalami mai dadi ya kasance shi ne yaren kaunarsu.
Toshewar hanyar sadarwa tsakanin ma’aurata: Idan ya kasance ma’aurata na zaune lafiya, amma kuma babu wata cikakkiyar kafar sadarwa a tsakaninsu, daya bai san abin da dan uwansa yake ciki ba, to wannan zai haifar da babban gibi cikin rayuwar aurensu. Wata sa’in rashin sadarwa tsakanin ma’auratan mai asali ce, da ita suka fara rayuwar aurensu, wata sa’in kuma wani abu ne kan faru cikin zamantakewar rayuwar auren sai ta tsinke hanyar sadarwar tsakanin ma’aurata.
Misalin irin dangantakar auratayyar: Maigida ya dawo, uwargida ta yi masa sannu da zuwa ta kawo masa abinci, yana gama ci ya kunna rediyo ko talabijin, bai yi mata sannu da girkin da ta yi masa ba ballantana ya yaba gyaran gidan da ta yi; haka ita ma babu batun ta tambaye shi yanayin fitarsa ta ranar, ko ta yi masa godiya ta yaba da kokarin da yake. Ba a zama a yi ’yar hira ta wasa da dariya, ba su gaya wa juna damuwarsu da sauran makamantan misalai.
Da yawan ma’aurata yadda wasu ‘yan uwa ko kawayensu suka san sirrinsu, wadanda suke aure ba su sani ba; idan wata matsala ke damunsu, ko da kuwa mai nauyin sirri ce, kamar wacce ta danganci ibadar aure ba su iya fada wa junansu, sai dai su yi sirri da kawaye ko ‘yan uwa.
Akwai da yawan matan auren da ibadar aure azaba ce a gare su, amma ba su taba bari mazajensu su gane, sai dai su yi ta daurewa suna shan azaba shekara da shekaru. Akwai kuma matan da ba su samun gamsuwar ibadar aure, amma ba su iya sanar da mazan nasu halin da suke ciki, ko su bayyana musu irin abubuwan da suke so lokacin ibadar aure.
Akwai matan da suna jin tsananin bukatar mazajensu, amma ba su iya neman mazan nasu da bukata in ba su ne suka bukace su ba. Haka mazan ma, wani za ka ga akwai wani abu da yake so matarsa ta rika yi masa, ba ta yi din kuma bai sanar da ita ba, da sauran misalai da yawa.
To wannan duk rashin sahihiyar kafar sadarwa tsakanin ma’aurata ke haifar da su, da yawan matsaloli za su kau cikin rayuwar aure in dai akwai sahihiyar kafar sadarwa tsakanin ma’aurata, domin hakan ne kadai zai haifar da cikakkiyar fahimtar juna tsakaninsu, idan kuwa aka samu fahimtar juna, to wannan zai zama kamar rigakafi ne na kowace irin matsala da ka iya kunno kai cikin rayuwar aure.
Magani
•    Maigida shi ne ja-gaba kuma jagoran gidansa, shi ke shimfida duk dokar da ya so a bi cikin gidansa, saboda haka shi ya fi dacewa da ya tabbatar da tabbatuwar budaddiya kafar sadarwa tsakaninsa da iyalansa, idan kuma wannan kafa ta tsinke ko ta toshe, to shi ya kamata ya sake buda wata sabuwar kafar sadarwar a tsakaninsu.
•    Ma’auratan da ke da irin wannan matsala ta rashin kafar sadarwa a tsakaninsu, yana da kyau su magance ta tun kafin ta yi nisan da magance ka iya zama sanadiyyar bullowar wata barakar kuma. Duk wata damuwa, ko wani hali da daya ke ciki sai ya daure ya sanar da dayan, ta haka sai su hada kai su nemi maganin matsalar tare. Idan ma akwai shakkar samun mummunan fahimta daga wanda ake auren, sai mutum ya zauna, ya yi nazarin matsalar da nazarin abokin zamansa, sannan ya yi nazarin hanya mafi dacewa ta sanar masa da wannan maganar ta yadda zai fahimta, kyakkyawar fahimta.
•    Sannan yana da matukar alfanu ga dukkan ma’aurata, hatta wadanda ke da kyakkyawar hanyar sadarwa tsakaninsu, ya kasance sun sanya wata rana, ko da karshen kowane wata ne, domin su zauna zama na musamman don tuntubar juna da nufin sanin matsalolin da daya ko dukkansu ke ciki, don a samo hanyar magance wannan matsala, kasancewar a rayuwa irin ta auratayya abin da ya shafi daya kamar ya shafi duka ne. Don haka maigida ne zai jagoranci irin wannan zaman tattaunawa da tuntubar juna, kuma har yaran gida yana da kyau a sa su ciki, sannan ya kasance an ba kowa cikakkiyar damar tofa albarkacin bakinsa don gano sababbin hanyoyin da za a bi wajen ciyar da gidan gaba da karin jin dadin zamantakewa da soyayya.
Mu lura, ko manyan kamfanoni da ma’aikatu ba su ci gaba ba sai da irin wannan zaman tuntuba da tattaunawa, to kuwa ba kamfanin da ya kai kamfanin gida da iyali, komai da komai na mutum a nan yake, hatta hanyar samun tsira ranar gobe kiyama, da fatan Allah Ya sa mu dace amin.