✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar rayuwa: Wata ’yar fim ta rataye kanta

Wata shahararriyar ’yar fim a kasar Indiya, Jiah Khan ta rataye kanta kuma ta sheka barzahu, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar.’Yar fim din, wacce…

Wata shahararriyar ’yar fim a kasar Indiya, Jiah Khan ta rataye kanta kuma ta sheka barzahu, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar.
’Yar fim din, wacce aka fi sani da lakanin Nafisa Khan, ’yar shekara 25 ce da haihuwa kuma kamar yadda rahoto ya tabbatar, ta rataye kanta ne a gidanta da ke unguwar Juhu da ke birnin Mumbai, Indiya.
Tun da farko dai, kafin marigayiyar ta dawo Indiya da zama, ta taso ne a kasar Ingila a kuruciyarta. Daga bisani ne kuma ta yanke kudurin dawowa Mumbai da zama tare da mahaifiyarta mai suna Rabiya.
Kamar yadda wata majiya ta kusa da marigayiyar ta fada: “Jiah ta kasance cikin damuwa a sanadiyyar matsalolin rayuwa na kashin kanta. Duk da haka ta takura wa kanta cewa sai ta dawo harkar fim tsundum, wanda haka ya sanya aka ga tana yawan zuwa wuraren masu shirya fina-finai domin samun tabbatar da kudurinta.”
Kamar yadda ’yan sanda suka fada, suna binciken maigadi da hadimarta da wasu makwabtanta, domin yi musu tambayoyi da nufin binciken gano bakin da suka ziyarce ta na karshe, kafin faruwar wannan abin takaici.
A ci gaba da bincikensu, ’yan sanda sun gano cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare kuma ba ta bar wata takardar wasicci ba. Tuni suka kai gawarta zuwa Asibitin Cooper domin binciken likita.
A game da sana’arta kuwa, Nafisa Khan ta fito cikin fina-finai masu dan dama. A 2007 ta fara fitow cikin fim din Nishabd tare da Amitabh Bachchan. Ta kuma fito cikin fim din Ghajini tare da Aamir Khan, kamar kuma yadda ta taka rawa a fim din Housefull tare da Akshay Kumar. A sanadiyyar kokarinta ne ma mujallar Filmfare ta taba karrama ta a matsayin kwararra.
A yayin da yake nuna alhininsa da mutuwarta, Tanuj Garg na kamfanin Balaji Telefilms, wanda kuma aboki ne a gare ta, ya ce: “Mun san juna ni da ita sosai, domin kuwa mukan tattauna al’amuran rayuwa da ita saboda mun hadu da ita ne tun a Landan. Ta kasance mai taushin murya, mai dadin mu’amala; ga ta kuma mai fahimta sosai. Babu shakka na kadu sosai da jin wannan mummunan labari na mutuwarta.”