✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsahi ya kashe abokinsa kan jayayyar shekarun haihuwa

Mazauna Unguwar Rafin-Sanyi da ke wajen garin Suleja a Jihar Neja, sun samu kansu a cikin alhini bayan da aka kashe wani matashi mai suna…

Mazauna Unguwar Rafin-Sanyi da ke wajen garin Suleja a Jihar Neja, sun samu kansu a cikin alhini bayan da aka kashe wani matashi mai suna Dikko Busa, wanda dan asalin yankin ne, kuma ake zargin cewa abokinsa ne ya daba masa wuka.

Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar makon jiya da dare, ya jawo tashin hankali a yankin, inda ya kai ga kona gidan iyayen wanda ake zargin bayan sulalalewarsa daga garin.

Aminiya ta samu labarin cewa rashin jituwa a tsakanin abokan biyu ta samo asali ne sakamakon jayayya a kan shekarun haihuwa lokacin da suke hira a wata mashaya; inda kowannensu ke ikirarin cewa ya girmi daya.

“Ana cikin haka ne sai wanda ake zargin ya dauki kwalba ya fasa sannan ya rika cakawa a cikin marigayin. An kai shi Babban Asibitin Suleja, inda aka tabbatar da cewa ya rasu,” inji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.

Bayanai sun ce tun a daren ne mahaifin matashin ya kai kansa ofishin ’yan sanda na Suleja don kare rayuwarsa sannan daga bisani ’yan sandan suka bar shi ya wuce da sharadin zai nemo dan nasa da ake zargi, mai suna Jibrin Zakari, wand dan asalin garin Auchi da ke Jihar Edo.

Dagacin yankin, Malam Zakari Madaki ya sanar da wakilinmu cewa yana gida kashegari bayan faruwar lamarin, bayan dawowarsa daga ofishin ’yan sanda, sai ga labarin cewa matasan sun banka wuta a gidan iyayen wanda ake zargi da kisan, inda ya kai ga konewar bangarensa.

Babban jami’in kungiyar ’yan sintiri na unguwar, Malam Sulaiman Yamawo ya ce ba a jima ba marigayin ya dauki belin wanda ake zargi da halaka sh daga wajensu, sakamakon tsare shi da suka yi bayan mahaifinsa ya kawo musu korafin cewa dan nasa ya yi masa duka a gida. “Bayan mun sake shi sai ya dauke shi zuwa wajen mahaifin nasa, inda suka nemi gafararsa tare sannan ya sasanta su,” inji shi.

Kwamadan ’Yan sanda na Shiyyar Suleja, ACP Isa Rambo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun mika lamarin ga sashinsu na binciken manyan laifuffuka da ke Minna, babban birnin jihar, don ci gaba da bincike a kan lamarin.