✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsafa sun kashe kananan yara biyu sun cire sassan jikinsu

A farkon wannan mako ne al’ummar Unguwar Hayin Gada da ke garin Saminaka suka wayi gari cikin alhini da tashin hankali, bayan da wadansu mutane…

A farkon wannan mako ne al’ummar Unguwar Hayin Gada da ke garin Saminaka suka wayi gari cikin alhini da tashin hankali, bayan da wadansu mutane da ake zargin matsafa ne, suka sace wadansu kananan yara biyu suka cire sassan jikinsu. Yaran masu suna Muhammad Isah dan shekara 10 da kanwarsa Zainab Isah ’yar shekara 2 bayan hallaka su matsafn sun cire sassan jikinsu ne kafin su watsar da su a wani kangon gida.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya faru, mahaifin yaran, Malam Isah Ahmed wanda aka fi sani da Ubaliyo ya ce, bayan ya tafi gona mahaifiyar yaran, ta  dauki waya ta ba su don su kai mata caji a bakin hanya da misalin karfe 11 na ranar da al’amarin ya faru.

Ya ce tunda suka tafi, sai aka ga ba su dawo ba, amma sai aka yi tunanin ko sun dawo sun shiga  makwabta ne. Ya ce da misalin karfe 12 na rana, sai aka nemi karamar yarinyar, aka tura makwabta amma ba a ganta ba.

Ya ce sai aka je wajen mai cajin, shi ma ya ce bai gansu ba, aka tafi nema, duk inda ya kamata amma ba a gansu ba, aka je wajen abokansa amma ba a gan su ba.

Malam Isah Ahmed ya ce sun je gidajen sarakuna da ofishin ’yan sanda na Saminaka da asibitocin cikin garin Saminaka sun bayar da cigiya, amma ba a samu labarinsu ba.

Ya ce sai da aka yi kwana hudu  da  misalin karfe 5 na yamma aka zo aka shaida musu cewa wani almajiri ya je bahaya a wani kangon gida, ya ga gawarwakin yara a wata unguwa mai suna Bakondi a nan garin na Saminaka.

“Da aka kira mu muka je muka duba sai muka ga yaran ne! Shi Muhammad tun daga fuskarsa sun kwaye ta sun cire idanunsa, fuskar dai baki daya sun kwashe ta kamar ba ta mutum ba. Ita kuma  Zainab baki daya abin da ya rage daga mararta ce zuwa kafofi, amma sauran rabin jikin sun tafi da shi, ba a gan shi ba,” inji shi.

Ya ce gaskiya ya shiga damuwa sosai sakamakon faruwar wannan lamari, domin tunda wannan abu ya faru, har zuwa lokacin da suke magana da wakilinmu, ba ya iya cin abinci.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, don jin ta bakin rundunar kan wannan lamari,  inda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce iyayen yaran sun kawo wa ’yan sanda rahoton bacewarsu, kuma sun yi bayanin cewa uwar yaran ce ta aike su, kuma tun daga nan ba a kara ganinsu ba, sai bayan kwana hudu aka gano gawarwakinsu an cire wasu sassan jikinsu.

Ya ce tun daga lokacin da aka gano gawarwakin yaran, ’yan sanda suka fara bincike don gano wadanda suka aikata wannan mugun aiki, ya ce kuma ’yan sanda na ci gaba da bincike don ganowa tare da gurfanar da wadanda suka yi wannan  danyen aiki a gaban kotu.