✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matata ce ta sa ni bidiyon barkwanci – Bello Galadanci

Fitaccen tauraron barkwanci a kafafen sada zumunta musamman Instagram da Tiktok Bello Galadanci ya ce ba don kuɗi yake bidiyonsa ba sai don ya fadakar…

Fitaccen tauraron barkwanci a kafafen sada zumunta musamman Instagram da Tiktok Bello Galadanci ya ce ba don kuɗi yake bidiyonsa ba sai don ya fadakar da nishadantar da masu bibiyarsa.

Galadanci ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da shirin Wata Sabuwa na tashar YouTube ta Aminiya Trust.

Ya ce  matarsa da suka haɗu a kafafen sada zumunta ce ta sa ya fara bidiyon barkwanci.