✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashiyar da ta yi karyar garkuwa da yi mata fyade ta shiga hannu

A baya na wallafa wani sako cewa an yi garkuwa da ni kuma an yi min fyade, duk karya ce, a yi hakuri.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Legas ta kama wata matashiya da ta yi karya cewa an yi garkuwa da ita tare da yi mata fyade.

Matashiyar da aka bayyana sunata Omotoyosi, ta wallafa a shafinta na Twitter mai suna @_misteriouss da misalin karfe 7:15 na safiyar Alhamis cewa ana garkuwa da ita da kuma yi mata fyade a lokacin.

Daga baya ma ta wallafa adireshi da kuma lambar wayar mutumin da ta ce yana garkuwar da ita.

“A halin yanzu an yi garkuwa da ni kuma ana yi min fyade a gida mai lamba 78 a titin Obayan da ke Pako Akoka a Jihar Lagos.”

Sai dai ta goge wannan sakon daga baya, tana mai neman afuwa a cikin wani bidiyo.

“A baya na wallafa wani sako cewa an yi garkuwa da ni kuma an yi min fyade, duk karya ce, a yi hakuri.

“A taimaka a daina yi wa mai lambar wayar barazana” a cewarta.

Aminiya ta ruwaito mai magana da yawun ’yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, na cewa tuni ta shiga hannu kuma suna bincike kan matashiyar.

Tun daga safiyar rabar Alhamis sunan Toyosi ke tashe a dandalin na Twitter sakamakon sakon da ta wallafa, inda akasarin masu amfani da shafin ke tofin Allah-tsine da abin da ta aikata.

%d bloggers like this: