✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya yi sanadin garkuwa da yara biyu ya shiga hannu a Katsina  

Wani matashi mai suna Aliyu Sani mai shekara 20, mazaunin Sabuwar Unguwa da ke cikin garin Katsina ya shiga hannun ‘ƴan sanda bisa zarginsa da…

Wani matashi mai suna Aliyu Sani mai shekara 20, mazaunin Sabuwar Unguwa da ke cikin garin Katsina ya shiga hannun ‘ƴan sanda bisa zarginsa da ake yi da hada baki tare da wani matashin mai suna Abdurrahman Danfulani (wanda ake nema ruwa a jallo) tare da sace wasu yara biyu da suke zaune a unguwa guda suka mika su ga masu garkuwa da mutane da ke cikin dajin yankin Batsari Safana.

Satar yaran Abubakar Muhammad mai shekaru 12 da Aliyu Ahmed mai shekaru 10 ya faru ne tun a cikin watan Afirilu na wannan shekara.

Kamar yadda Kakakin ‘ƴan sanda Sufeto Isa Gambo, ya shaidawa manema labarai, kame Aliyu ya biyo bayan wani samame da suka yi akan masu tu’ammali da miyagun kwayoyi inda aka kama shi da kwalebin sunadarin sha ayi maye. A cikin bincike ne suka gano cewar da ma an taba kawo rahotansa bisa zargin sace wadannan yara biyu amma ya boye sai yanzu ne ya shiga hannu.

Aliyu, wanda yake matashi ya ce yana gyaran babura, ya sami kansa a cikin aikata wancan laifi na sace yaran bisa yaudarar wancan aboki na shi da nufin zasu samu kudi. A karshe mahaifin Abubakar ya biya Naira dubu 150 aka sako masa yaro yayin da shi Aliyu Ahmed, ya tsere daga hannun matasan. Kamar yadda Aliyu ya ce, an basu Naira dubu 30 ne daga cikin kudin su ma abokin wato Abdurrahman ya gudu da su bai bashi ko sisi ba.