✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da aka tumbuke wa harce ya bukaci taimakon jama’a

A ranar 4 ga Oktoban shekarar 2017 ce wata mata ta datse wa wani matashi mai suna Babangida harce, lamarin da ya sanya aka kwantar da…

A ranar 4 ga Oktoban shekarar 2017 ce wata mata ta datse wa wani matashi mai suna Babangida harce, lamarin da ya sanya aka kwantar da shi asibiti, inda jami’an tsaro suka kama matar wacce a halin yanzu take gidan kaso na Kirikiri da ke Legas, kuma ake gudanar da shari’a a kan lamarin, a wata kotu, a garin Legas.

Aminiya ta dauko cikakken rahoton a can baya, yanzu kuma ta sake bibiyar labarin, domin jin halin da matashi yake ciki, inda wakilinmu ya ziyarci gidansu a Unguwar Ogudu a Legas.

Babangida Sulaiman wanda a lokacin yake shirin tafiya garin Zariya domin komawa makaranta, bayan kammala hutun zangon karatunsa a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu ya samu sauki kuma yana iya yin magana fiye da yadda muka same shi a baya. Kuma ya ce a yanzu yana iya cin abinci fiye da baya, sai dai ba ya iya cin abinci mai zafi. Ya ce yakan ci abinci a hankali, domin sau tari yakan kuskure ya ciji kansa a lokacin da yake cin abincin.

“Sannan ba kowace kalma nake iya furtawa ba, akwai kalmomin da ba na iya furta su. Kadan daga cikin haruffan da ba na iya furtawa sun hada da harufan ‘r’ da ‘k’ da kuma ‘z.’ A koyaushe burina in samu wanda zai dauki nauyin kai ni kasar waje domin a yi mini aiki in samu lafiya,” inji shi.

Ya ce tun bayan lokacin da ya warke ya samu gurbin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda a yanzu yake aji biyu na Difiloma kan nazarin Hulda Tsakanin Kasa da Kasa. Ya ce duk da gutsurewar harcen nasa, ba ya shafar kwazonsa a makaranta, amma yakan fuskanci kalubale da dama.

“Akwai salon karatun da za a bukaci dalibi ya fito gaban abokan karatunsa da malamansa, ya gabatar da mukala. Nakan fuskanci tarnaki a wannan fanni, kodayake akwai malamaina da dama da suke sane da halin da nake ciki, su kansu abokan karatuna sun san halin da nake ciki. Na yi mamakin ganin yadda kowa ya san da labarin abin da ya faru da ni. Domin a ranar farko da na samu kaina a makaranta a tsakanin dalibai na yi mamakin yadda abokan karatuna suka game cewa ni ne wanda aka cire wa harce, wasunsu daga sun ci karo da ni sai su tambaye ni, su kuma binciki hotona a yanar gizo domin su tabbatar,” inji shi.

Babangida Sulaiman ya ce babban burinsa shi ne ya samu tallafi ko wanda zai dauki nauyinsa a yi masa aiki a kasar waje. Kuma yana son ganin kotu ta hukunta matar da ta cire masa harce gwargwadon laifin da ta aikata.

Aminiya ta zantawa da mahaifiyar matashin mai suna Hajiya Hassana, wadda ta ce har yanzu suna ci gaba da zuwa sauraron shari’ar. “Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne na rashin kudi, duk abin da nake da shi ya kare a wajen shari’ar. Yanzu haka ranar 6 ga watan gobe za mu je kotu kamar yadda kotun ta sanar mana, sai dai a yanzu haka lauyan da ke kare mu yana bi na Naira dubu 40 cikon kudin aikinsa kuma ya ce in ban samo su ba, ba zai zo sauraron shari’ar ba. Wannan kadan daga cikin kalubalen da muke fuskanta a wannan lamari ke nan.

Mutane da dama sun yi yunkurin taimaka mana ta fuskar shari’a da kai yaron kasar waje domin a yi masa aiki amma lamarin ya ci tura, har yanzu ba a kai ga gaci ba. Don haka ina kira ga jama’a duk mai halin tallafa mana, ya zo ya taimake mu domin muna bukatar taimako,” inji ta.

Ta ce zuwa yanzu matar da ta tumbuke harcen dan nata na kurkukun Kirikiri kuma daga nan ake kawo ta kotu. A can baya an ba da belinta amma ta gaza cika ka’idojin belin, lamarin da ya sanya har yanzu ake tsare da ita a gidan kaso.