Wata kotun Majistare mai zamanta a Ota, Jihar Ogun, ta ingiza keyar Gideon Michael dan shekara 29, zuwa gidan yari na wata uku bayan da ta kama shi da laifin satar wayar salula mai darajar N30,000.
Kotun ta kuma sa Michael ya biya mai wayar tsabar kudi Naira N35,000 bayan da mai tuhuma ya gamsar da ita kan laifin da ya aikata.
- Za mu yaki sayen kuri’a a zaben Osun —Jami’an tsaro
- Yadda Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan N225 a shekara 20
Alkalin kotun, A.O. Adeyemi ya yanke wa matashin hukuncin zaman kaso na wata uku ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu 10.
A lokacin da yake yi wa kotun bayani, lauyan mai gabatar da kara, E.O. Adaraloye, ya fada wa kotun cewa Michael ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1:30 na rana a yankin Okitikan Ota, inda Michael din ya sace waya mai darajar N30,000 mallakar wata mai suna Mary Adelegan, kuma ya lalata wayar.
Adaraloye ya ce laifukan sun saba wa sassa na 390 (9) da 451 na Kundin Dokokin Ogun na 2006.