✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya kashe budurwarsa, ya cinna wa kansa wuta

Matashin ya zargi budurwar kan cin amanarsa da wani.

Wani matashi ya rataye budurwarsa sannan ya cinna wa kansa wuta a yankin Kom Kom da ke Karamar Hukumar Oyigbo ta Jihar Ribas.

Wata majiya ta shaida cewar matashin mai inkiyar Baby Face ya gayyaci budurwar ta shi ce zuwa dakinsa a karshen mako.

“Al’amarin ya faru ne a karshen mako a yankin Kom Kom na Oyigbo.

“Wani matashi ne ya samu sabani da budurwarsa kan zargin cewa tana cin amanarsa ta hanyar kula wasu samarin.

“Ya yi wa marigayiyar dukan tsiya sannan ya shake ta.

“Bayan da ya samu nasarar kasha ta, sai ya kone gidansa a matsayin wani yunkuri na hana gane abin da ya faru,” in ji majiyar.

Majiyar ta ce bayan da budurwar ta gaza kare kanta daga zargin cin amana da saurayin ke yi mata, hakan ya sa ya shake ta har sai da ta mutu.

Daga baya ya rataye gawarta saboda gudun kada a gano abin da ya aikata, sannan ya cinna wa gidan wuta.

Majiyar ta ce lamarin ya haifar da firgici a yankin, yayin da mazauna unguwar suka tsere saboda gudun shiga hannun ‘yan sanda.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko, ta ce har yanzu ba ta da masaniya kan faruwar lamarin.

%d bloggers like this: