✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya hallaka iyayensa ya soki kanwarsa da wuka

Rundunar ‘yan sanda a Legas na farautar wani matashi dan shekara 23 da ya hallaka mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuma dabawa ‘yar uwarsa da ke…

Rundunar ‘yan sanda a Legas na farautar wani matashi dan shekara 23 da ya hallaka mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuma dabawa ‘yar uwarsa da ke aikin yi wa ƙasa hidima wuka.

Ana zargin wanda ake nema ruwa a jallon mai suna Michael Okhide, da kashe mahaifinsa mai shekara 60 mai suna Barista Clement Okhide da mahaifiyarsa Toyin Okhide, kana ya dabawa ‘yar uwarsa wuka wacce ta shigo gidan ta tarar da aika aikan da ya yi, sai dai ita ta tsallake rijiya da baya, inda ta ruga a guje domin tsira da ranta.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa, lamarin ya auku ne a unguwar Gbadamosi da ke yankin Ejigbo a ranar Talata da ta gabata.

Zuwan ‘yar uwar tasa na samun kulawa a asibitin Ejgbo, yayin da aka kai gawarwakin iyayen nasa dakin ajiyar gawa, wasu ‘yan unguwar da lamarin ya abku sun shaida cewa matashin na fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.