Hukumar Kula da Ilimin Sana’o’i da Kimiyya da Fasaha a Najeriya NBTE, ta ce akwai matasa kusan miliyan 90 da yanzu haka basu da ayyukan yi a cikin kasar, cikin su har da wadanda suka kammala karatun digiri a jami’o’i.
Shugaban hukumar, Farfesa Idris Muhammad Bugaje ya kuma ce daga cikin wannan adadi, akwai matasa miliyan 10 da basa zuwa makaranta baki daya, kuma akasarinsu almajirai ne da ke yawon bara.
- Abin da ya sa na fice daga PDP —Abba Gida-gida
- Saudiya da Qatar sun koka kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya
Bugaje ya danganta matsalar tsaron da ta addabi Najeriya da rashin ayyukan yi wanda ya mamaye sassan kasar, yayin da ya bukaci gwamnati da ta mayar da hankali wajen koyar da ilimin sana’o’i ga matasa domin dogaro da kai.
Shugaban hukumar wanda yake jawabi a wurin Babban Taron shekara-shekara na Kungiyar Kimiyya da Fasaha ta STF a Jihar Kaduna, ya ce akwai matasa da dama da suka kamala karatun jami’a kuma suke dauke da shaidar mallakar digiri amma kuma basu da aikin yi.
Bugaje ya buga misali da kasar Bangladesh wadda ke koya wa matasanta ilimin sana’o’i, abin da ke ba da damar kai su kasar Saudi Arabia domin yin aikace-aikace a bangarori da dama, abin da ke taimaka wa kasar samun kudaden waje.
Shugaban hukumar ya bayyana damuwa a kan kungiyar matasan da ake samu a Jihar Kano, wadda ta yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su, saboda haka za su lalata kadarorin da ta mallaka a sassan jihar.
A kan haka ne ya bukaci daukar matakan gaggawa kafin kungiyar matasan ta yi karfi yadda za ta zama wata babbar barazanar tsaro a kasa baki daya.