Hajiya Asma’u, matar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, marigayi Alhaji Shehu Malami, ta maka ’ya’yansa a kotu kan rabon gado.
Wadanda Hajiya Asma’u da ’ya’yanta biyar suka maka a gaba kotun ’ya’yan mijin nata ne, Aminu da Hafsah, saboda kadarori da kuma wasiyyar da mamacin ya bari.
Sauran waɗanda suka shigar da ƙara sun haɗa da: Mustapha, Sadiƙ, Amina, Zainab da A’isha, ’ya’yan marigayi Malami da Asma’u.
Masu karar suna neman wadanda ake kara su yi bayanin inda wasu kadarorin mamacin da ke Abuja da kuma Mambila a Jihar Taraba.
- Majalisar Kaduna ta kafa kwamitin binciken Gwamnatin El-Rufai
- Yadda ake rubutun sha ɗan kamfani a Turai
A zaman na ranar Talata, alkalin kotun, Alkali Nasiru Jibdawa, ya karba tare da yin tambayoyi kan wasiyyoyin biyu da marigayi Malami ya bari, wadanda wani shaida mai suna Alhaji Abdulkadir Bello ya gabatar a gabansa.
Lauyan masu ƙara, Malam Nasiru Shehu-Na’ige, ya roƙi a yi musu bayanin inda wasu gidaje mallakin mamacin a unguwar Maitama suke .
Haka kuma suna neman bayanin inda wasu filayensa a wasu wurare a Abuja da kuma gonarsa da gidansa da ke Mambila a Jihar Taraba suke.
Bello, wanda ya shaida wa kotun cewa yana ɗaya daga cikin masu kula da kadarorin da wata kotu a Abuja ta nada, ya bayyana cewa marigayi Malami da kansa ya sayar da filayensa da ke unguwannin Asokoro da Guzape a Abuja.
Amma kuma, Bello, wanda dan uwa ne ga marigayi Malami ya bayyana cewa bayan rasuwar mamacin ne aka sayar da gonarsa da gida da ke Mambila.
Shaidan ya kara da cewa gidan da ke Maitama Abuja da kuma a Alkammawa, Jihar Sakkwato a suna cikin wasiyyar da marigayin ya bari.
Bello ya ƙara samar da bayanan kaddarorin marigayi Malami da ke jihohin Kaduna da Kano da Sakkwato tare da hannun jarin da ke cikin kamfanoni daban-daban da darajar su a kasuwa da asusun banki.
Haka kuma ya bayyana cewa ana ƙoƙarin karbo gidajen mamacin da ke kasar Masar.
Lauyan wadanda ake kara ya shaida wa kotun cewa zai yi masa tambayoyi ne bayan bangaren masu kara sun gama nasu.
Amma ya tabbatar cewa wasiyyoyin na dauke da bayanai da suka dace kuma wadanda aka ba wa alhakin kula da kadarorin su ne mata da kuma ’ya’yan mamacin.
Bayan sauraron bangarorin ne kotun ta dage ci fa da sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan nan na Afrilu.