Uwargidan Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, Fasto Patience Umo Eno, ta rasu.
Matar Gwamna Umo Eno ta rasu ne a asibiti a yayin da ake jinyar ta sakamakon rashin lafiya.
Gwamna Umo ne ya sanar da rasuwar mai ɗakin tasa ne kafin wayewar garin ranar Juma’a.
Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Ini Ememobong, a cikin sanarwar da ya fitar a safiyar Juma’a ya ce Fasto Patience ta rasu ne a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa duk da rasuwar, gwamnan yanba wa al’ummar jihar cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hidima wa al’umma.