✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato

Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har ragunan suna uku da buhunan abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira…

Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar.

Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin.

Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar.

A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin sada zumunta, Nasir Bazza, ya fitar, ya ce mutanen ƙauyen sun yi farin cikin ganin matar gwamna a garin, wanda shi ne karo na farko da suka ga matar gwamna a yankin nasu.

Ya ce matar gwamna ta yi alkawalin ci gaba da bayar da irin wannan tallafi ga duk wata mata da Allah ya albrkace ta da samun karuwar ’yan uku a lokaci guda a jihar.