✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da mijinta ya yi kokarin zubar mata da ciki ta haifi ’yan 4

Sai dai mutumin ya nemi a taimaka masa

Wani mutum da ya yi yunkurin zubar da cikin matarsa lokacin da take da juna-biyu, a ranar Alhamis din da ta gabata ta haifi jarirai ’yan hudu a garin Ogbomosho na Jihar Oyo.

Mutumin, mai suna Dauda Olamilekan mai shekara 30 da ya ce matarsa mai suna Rukayat mai shekara 27, ta haifa masa ’ya’yan a lokacin da ba shi da hali, inda ya nemi a taimaka masa.

Ya roki Gwamnati da jama’a masu hali su taimaka masa domin a cewarsa ba shi da kudin da zai iya daukar dawainiyar wadannan jarirai.

A lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a harabar cibiyar kiwon lafiya ta Baaki, inda Rukayat ta haihu, Dauda Olamilekan da yake sana’ar Fawa ya ce ma’aikayan asibitin ne ma suka hana shi zubar da cikin a baya.

Ya ce, “Kafin isowar wannan lokaci, mun taba zuwa daukar hoton cikin matata Rukayat a cibiyar lafiya ta Genesin da ke Ogbomoso, inda jami’an kiwon lafiya na cibiyar suka shaida mana cewa jarirai 4 ne a cikinta.

“A nan take na yanke shawarar daukar matakin zubar da wannan ciki domin ba ni da kudi, ba zan iya ba. Amma jami’an cibiyar suka hana ni daukar wannan mataki.

“Su ne suka taimaka mana har zuwa ranar Alhamis da Rukayat ta haifi wadannan jarirai 4,” in ji Dauda.

Aminiya ta ce har zuwa lokacin rubuta wannan labari wadannan jarirai 4 maza 2 mata 2 na cikin koshin lafiya a Asibitin koyarwa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso.

Kafin ta haifi wadannan jariran, Rukayat da mijinta Dauda da suke zaune a unguwar Ijeru suna da ’ya’ya 2 da yanzu haka suke raye a duniya.