✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar aure ta yi hayar wasu maza sun kashe mijinta akan Naira dubu 150

Wata mata jami’ar kiwon lafiya a jihar Ribas ta bayyana yadda ta yi hayar wasu maza biyu suka kashe mijinta biyo bayan sabanin da ya…

Wata mata jami’ar kiwon lafiya a jihar Ribas ta bayyana yadda ta yi hayar wasu maza biyu suka kashe mijinta biyo bayan sabanin da ya shiga a tsakanin su

Matar mai suna Ajamine mai shekaru 41 da ‘ya’ya 4 ana zargin tane da hada kai da wasu maza 2 suka kashe mijinta Inedugoba Tyger.

Marigayin Inedugoba Tyger

Rundunar ‘yan sandan ta musamman Dame karkashin ofishin babban Sufetan ‘yan sanda na IRS ne suka kame matar tare da abokan aika-aikan nata bayan da dan uwan marigayin ya aike da takardar koke zuwa ga hukumar ‘yan sandan kasa.

Matar ta shaida cewa, ta yi hayar mutum biyu da suka hadar da Kinsely Nna da abokin sa Sunny wadanda suka kashe maigidan nata,  ” mun sami sabani da mijina tun bayan da ya fara nuna mini wasu miyagun dabi’u sakamakon rasa aikin sa da ya yi ya shiga cikin damuwa da yawan fada, inda yake yawan kyararta har muka yi fada ya bar gidan kafin daga bisani muka sasanta”.

Ta ce mijin nata na yawan kyaranta kana yana yimata fyade a duk sanda sha’awar sa ta taso mata sai ya neme ta da karfin tsiya lamarin da ya sanya wani lokacin da yazo mata sai ta kira Nna wanda ya je da abokinsa suka lakadawa mijin nata duka har ya rasa ransa.

“Da suka kashe shi sun yi min kashedi cewa, kada na sake na fadawa kowa inda suka yi barazanar kashe ni da ‘ya`yana idan na sake na faxa, sai muka saka shi a rami muka rufe, daga nan na sayar da wayar salular sa akan Naira dubu 15, Kinsely ya tambaye ni kudi na ba shi Naira dubu 150 daga nan ya ci gaba da zuwa yana saduwa da ni kafin daga nan a ‘yan sanda suka kama ni”. In ji ta.

A nasa bangaren daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Kinsely Nna, ya shaida cewa Naira dubu 100 matar ta biya su shi da abokin sa domin su yi wa mijin nata dan karen duka, ya ce ita ta tursasa su suka kai ga aikata laifin.