Matar shahararren dan sanda, DCP Abba Kyari, da ke fuskantar zargin fataucin hodar Iblis ta yanke jiki ta fadi a sume a kotu.
Matar tasa mai suna Ramatu Kyari, ta sume ne a yayin da aka sake gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a safiyar Litinin kan zargin fataucin hodar Iblis.
- Shugaban Kwamitin Binciken Abba Kyari ya rasu
- ‘Akwai yiwuwar ASUU ta zarce da yajin aikinta har sai abin da hali ya yi’
Ta sume ne jim kadan bayan alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya dage yanke hukunci kan bukatar da Abba Kyari da suaran mutane shida da ake zargin su tare suka gabatar na bayar da belinsu a gaban kotun.
Alkalin ya dage zaman ne zuwa ranar 28 ga watan Maris, ya kuma umarci Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da ke karar su ta ci gaba da tsare su.
Alkalin kotun ya sanar da haka ne bayan Hukumar NDLEA ta nemi kotun ta yi watsi da bukatar, tana zargin idan aka ba da belin su, za su iya tserewa da Najeriya ko su ki halartar zaman kotu.
Jami’an NDLEA na wucwea da mijin nata da sauran takwarorinsa daga kotun bayan zaman ne aka ga Ramatu ta yanke jiki ta fadi a kasa.
Wata daga cikin matan da suka zo kotun tare ta bayyana wa kafar yada labarai ta Channels cewa Ramatu na fama da cutar Asma.
Sauran mutum shida da ake zargin Abba Kyari tare da su ’yan sanda ne — ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Inspectors Simon Agirigba, John Nuhu, dai kuma ASP John Umoru wanda ya tsere.
Akwai kuma Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne wadanda su kuma sun aikata laifin da ake zargin su da aikatawa, amma sauran biyar din sun musa laifina.