✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Najeriya za su hadu da Brazil da Ingila a gasar cin kofin duniya

kungiyar kwallon kafa ta mata ta ’yan kasa da shekara 17 ta Najeriya da ake wa lakabi da Flamengos za ta kara da kasashen Brazil…

kungiyar kwallon kafa ta mata ta ’yan kasa da shekara 17 ta Najeriya da ake wa lakabi da Flamengos za ta kara da kasashen Brazil da Ingila da kuma Koriya DPR a gasar cin kofin kwallon kafa na mata da zai gudana a Jordan. Su dai ’yan matan an kasafta su ne a rukunin C, rukunin da ake ganin ya fi kowane rukuni zafi.
Jadawalin da Hukumar shirya kwallon kafa (FIFA) ta fitar ya nuna rukunin A ya kunshi mai masaukin baki Jordan da Sifen da Medico da kuma New Zeland ne, yayin da rukunin B ya hada kasashe irin su benezuela da Jamus da Kamaru da kuma Kanada.  Rukunin C ya kunshi Najeriya da Brazil da Ingila da kuma Koriya DPR.  Sai rukunin D da ya kunshi Amurka da Paraguay da Ghana da kuma Japan.  Kenan kasashen Najeriya da Kamaru da Ghana ne za su wakilci Nahiyar Afirka a gasar.
Za a fara gudanar da gasar ce a ranar 30 ga Satumba zuwa 21 ga Oktoban wannan shekara a Jordan.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya za ta halarci gasar tun bayan da aka fara a shekarar 2008.
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Flamingo Bala Nikyu ya ce sun shirya tsaf don tunkarar gasar kuma yana fata ’yan kwallonsa za su ba marada kunya.