✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan aure da aikin gwamnati: Faduwa ko riba?

Mafi yawa daga cikin matan da suke zage damtse don su yi karatu babu wani burin da ke ransu face, idan sun gama su fara…

Mafi yawa daga cikin matan da suke zage damtse don su yi karatu babu wani burin da ke ransu face, idan sun gama su fara aikin gwamnati a dama da su. Da za a tambayi wacce take karatun lakita mene ne burinta abin da za ta ce shi ne “in zama likita” haka idan aka tambayi mai karatun lauya ita ma za ta ce tana son zama lauya, yawanci duk wadda aka ga tana karatu ba tana yi ba ne saboda muhimmancinsa ba ne kawai, a’a, tana yi ne don kwadayin idan ta gama ta samu wajen da za a raba don cin moriyar karatun da aka yi.
Ina so mata su fahimci ba wai ina kushe karatunsu ko kuma aikin da suke yi ba ne, kasancewar ilimin ‘ya’ya mata yana da matukar muhimmanci, domin mata su ne suke zaune a gida tare da ‘ya’ya; su ne suka fi sanin shige-da-ficensu, dalilin da ya sa idan suka kwankwandi ruwan ilimi ba karamin ci gaba za a samu ba. Na farko mace mai ilimi tana da dabarun zama da miji, ta san yadda za ta tarairaye shi; ko da laifi ta yi masa ta san yadda za ta saukar da shi cikin hikima da kisisina. Ba ya ga haka macen da ta samu ilimi ‘ya’yanta ma da ilimi za su taso, domin za ta zama malamar ‘ya’yanta wajen koyar da su darussan da ba sa ganewa a makaranta da abin da ya danganci tsafta da kuma tarbiyyarsu. Duk wadannan ci gaba za su samu ne idan aka samu mace mai ilimi da jajircewa a gidan mijinta.
Ashe idan muka kalli wadannan abubuwa za mu iya cewa karatun ‘ya’ya mata abu ne mai matukar muhimmanci, sai dai wani abu da nake lura da shi, shi ne, yanzu mafi akasarin mata ba wannan ne ajandar da ya sa suke dagewa zuwa karatu a kwalejoji da jami’o’i ba, suna yi ne kurum don kwadayin aikin gwamnati. Da wuya a samu macen da ta yi difloma ko digiri ta zauna ta ce ba don aiki ta yi karatunta ba, ko da akwai su to na tabbata ba su fi cikin cokali ba.
Da yawa ba sa tsayawa su yi nazarin cewa shi fa arziki na Allah ne, ba dole sai da aikin gwamnati ake samun rufin asiri ba, idan mace ta tsaya ta yi sana’a a gidanta ya fi mata dacewa fiye da ta rika zirga-zirga a kan titi zuwa wajen aikin da take tutiya. Ina mamaki ta yadda macen malam Bahaushe za ta dage kan sai ta yi aikin gwamnatin a gidan mijinta, ba tare da tana la’akari da mijin yana bukatar hakan ko ba ya bukata ba, sannan ba ta la’akari da shi kansa yanayin aikin da za ta yi, kawai tana kudurta abin da za ta samu idan wata ya yi, to fa shi ke nan burinta ya cika.
Allah Ya sa kada mata masu aikin gwamnati su yi mini mummunar fahimta, domin na rubuta wannnan makalar tawa ce dangane da matan aure masu aikin gwamnati da suke yi wa aurensu rikon sakainar-kashi. Ina mamakin yadda taura biyu za ta taunu a baki, kamar yadda Hausawa suke fada ba a hada gudu da susar duwawu, idan na kalli mace wadda take rayuwa a gidan mijinta kuma ga aiki tana yi sai in ga ai babu yadda za ta iya fitar da hakkin kowanne kamar yadda ya kamata.  Yaushe za ta kula da ‘ya’yanta da kuma kulawa da mai gidanta ba tare da mai gidanta ya kosa ba? Amsar dai na san ita ce, in dai ana son a yi ibadar aure yadda ta dace, to sai dai a rika yi wa aikin sama-sama, duk da na san ba haka aka so ba.
Na tabbata daga cikin magidantan da suke rayuwa irin wannan da matansu da za ka tambaye su yadda suke rayuwa sai ka sha mamaki, domin kuwa wannan ba bakon abu ba ne cikin unguwanninmu da garuruwanmu.
Daga cikin matsalolin da suke faruwa a irin wannan yanayi sau da yawa matar mutum ita ke riga shi fita wajen aiki, sakamakon fitar ta da wuri ba lallai ta kammala ayyukan da suka cancanci ta yi da safe ba, sannan watakila shi zai riga ta dawowa, nan ma kuma ya dawo ga gajiya ga yunwa amma haka zai zauna yana hamma yana jiran sai madam ta dawo zai ci abinci, to haka abin yake ko akwai ‘ya’ya su ma haka za su rika shan wahala, sun dawo daga makaranta ba su tarar da mahaifiyarsu ba, daga nan sai su shiga gidaje su koyi kwalama; mafi yawancinsu ba sa taimaka wa mazajensu da komai, hatta kudin da suke samu ba sa bari mazajensu su san ma’ajiyarsu, abin da ke gabansu shi ne kayan daki da gudunmawar biki, domin ni shaida ne na ga macen da ta ninka mijinta albashi amma ba ta taba taimakonsa da ko naira daya ba, hatta kudin makaranta na yara idan ta ranta ba ya nan, to idan ya dawo sai ta fada masa ya biya ta. Irin wadannan misalai suna da yawa.
Babban misali da nake son bayarwa a nan shi ne, mafi yawan matan da suke aikin gwamnati sun raina mazajensu ba su dauke su a bakin komai ba, suna ganin idan ma an sake su ba wata tsiya ba ce, tun da suna da madogara, mazajen da suke rayuwa da matansu a wannan yanayi su kadai suka san irin bacin ran da suke fuskanta, domin kallon kitse kawai ake yi wa rogo.
Babban abin bakin ciki shi ne yadda kana kallo a gabanka matarka za ta fito ta tafi cikin abokan aiki wadanda ba muharramanta ba, duk mai kishin matarsa ba zai so ta kebanta da wani ba, idan ba dan uwanta ba. Idan muka kalli nasararorin da kuma matsalolin, to za mu ga babu riba sai dai faduwa.
Shawara:  na farko duk matar da za ta yi aiki, to ta ji tsoron Allah ta tabbata tana kula da hakkin mai gidanta da na ‘ya’yanta, ta kuma ji tsoron Allah wajen kamewa, ko ta rungumi sana’a a gida.
Allah Ya sa mu dace, Ya ba mu rufin asiri duniya da lahira, amin.
Ibrahim IBB ya rubuto daga Kazaure, Jihar Jigawa, za iya  a wannan lambar: 07031616267