✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Arewa 540 sun fara samun horo a kan kiwon kifi

Kimanin mata 540 ne da suka fito daga yankunan jihohin Arewa 19 na kasar nan ke samun horo a kan kiwon kifi karkashin wani shirin…

Kimanin mata 540 ne da suka fito daga yankunan jihohin Arewa 19 na kasar nan ke samun horo a kan kiwon kifi karkashin wani shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Jihar Kano da kuma ta tarayya.
Aminiya ta kalato cewa  za a dauki tsawon makonni uku ana gudanar da wannan horo a Makarantar Koyon Kiwon Kifi da ke Bagauda cikin Jihar Kano.
Da take kaddamar da shirin, Kwamishinar Noma da Albarkatun kasa ta Jihar Kano, Hajiya Baraka Sani ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki nauyin mata 140 daga cikin adadin da za a ba horon, wanda bayan kammala shi za a ba kowacce daga cikin matan jari da irin kifi da abincinsu da magunguna da sauran kayayyakin da za su taimaka wajen aiwatar da sana’ar kiwon kifin.
Hajiya Baraka ta ci gaba da cewa akwai wasu karin shirye-shiryen hadin gwiwar tsakanin gwamnatin Kano da ta tarayya, inda za a ba matasa horo a kan kiwon kaji da dabbobi.
A nata banagaren wakiliyar ma’aikatar ayyukan gona da raya karkara ta kasa, Hajiya Karimatu Babangida ta yaba wa kokarin gwamnatin Kano na bullo da wannan shiri, wanda ta ce zai taimaka wajen rage makudan kudin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da kifin da ake bukata. “Wannan shiri zai taimaka wa gwamnatin kasar nan wajen rage kudin da take kashewa don shigo da kifi daga kasashen waje. A duk shekara Najeriya kan kashe Naira biliyan 90 wajen shigo da kifi don samar da adadin ton biliyan uku na adadin kifin da ake bukata a kasar nan.” Inji ta.