Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
2. Tsare Farji: Kamar yadda ya zo a bayanan da suka gabata, Allah SWT ya yi wannan umarni ga Mata Musulmi a cikin Aya ta 31, Suratun Nur:
“Kuma ka ce ga Mu’uminai mata su runtse daga gannansu kuma su tsare farjojinsu; kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta…”
Yake ’yar uwa mai albarka; ki sani, Allah ya yi wannan umarni gare ki ne don Ya tsarkake ki daga alfasha da kuma munanan dabi’u; kuma don hakan ya zama kariya ga jikin da nafsinki da sarke-sarken zuciyar mazan da ba muharramanki ba. Tsare farji daya ne daga cikin dabi’o’in Mu’uminai wadanda Allah Ya siffanta su da su cikin Littafinsa mai Tsarki; kuma Ya bayyana cewa dabi’a ce da ke gadar da nasara da rabo mai girma ga mu’uminai a rayuwar duniya da lahira. A bayyane yake cewa duk wata nasara da daukakar da ’ya mace za ta samu a rayuwa, to yana bayan samun nasara a gidan aurenta; duk kuwa wacce ta samu nasara a gidan aurenta; to ana kyautata zaton za ta dace da cin nasarar ranar gobe kiyama.
Tsare farji muhimmin abu ne da zai ba mace nasara da daukaka a rayuwar duniyarta da lahirarta; don haka ya kamata duk wata uwargida tagari mai fatan samun irin wannan nasara da daukaka ta dage wajen bin wannan umarni na Allah SWT don ganin ta dace da samun nasara da babban rabo a rayuwar duniya da lahira. Mu fahimci cewa wannan umarni ne da ya shafi matan Musulmai duka masu aure da ’yan mata.
Matakan Tsare Farji: Mace Musulma za ta tsare farjinta ta hanyoyi guda uku:
I. Tsari Na Tufa: Watau mace Musulma ta tsare al’aurarta da tufafi, ta hanyar sakaya ta daga ganin idon mutane; wannan na nufin duk wata tufa da in aka sanya ta za ta bayyanar da surar jikin ’ya mace, musamman ta saman kirjinta; mazauna; da kuma kasan mararta; bai halatta ta bayyana kanta sanye da irin wannan tufa ba ko da kuwa ga mutanen da suke muharramanta ne, watau mahaifanta ko ’ya’yanta.
II. Tsare Motsuwar Sha’awa: Wannan na nufin mace Musulma ta tsare farjinta daga motsuwar harammataciyar sha’awa a cikinsa. Lallai kada ta yi sakacin barin wani jin dadi na motsuwar sha’awa ya motsu a cikin gabar farjinta, ko a wata gaba daga cikin gabobin sha’awar jikinta face sai in mijin aurenta ne kadai ya zama dalilin motsuwar wannan sha’awa, wannan ne ya sa aka fara gabatar da maganar tsare ganin ido kafin tsare farji, domin kafin motsuwar sha’awa, akwai wasu abubuwa da kan faru har su zama musabbabin motsuwar sha’awa, kuma gani shi ne mafi tasiri a wajen motsuwar sha’awa sama da sauran kafofin hankali kamar yadda ya gabata. Da zarar ganin ido ya dira akan abin da ya burge zuciya, take sha’awa za ta motsu a zuciya da gabobin sha’awa. Don haka dole uwargida ta tsare kanta daga dukkan wani aiki, komai kankantarsa, ko da kamar girman kwayar zarra ne, wanda in tsautsayi ya gifta, zai iya zama sanadiyyar motsuwar haramtacciyar sha’awa.
III. Tsare Makaman Sha’awa: Ya ’yar uwa mai albarka, kamar yadda kika runtse ganinki daga yawan kalla-kallacen mazan da ba Muharramanki ba, wanda hakan ya zama tsari ga farjinki, to haka zaki dage ki tsare jikinki da dukkan wata siffa taki daga zama abin sha’awa, abin kayatar da duk wani namijin da ba mijinki ba; wannan shi ne dalilin umarnin cewa ki boye adonki domin bayyanar da shi zai zama fitina ga mazaje da yawa, kuma zai iya zama cutarwa gare ki in tsautsayi ya gifta. Don haka ki zama mai kishin kanki, kada ki yadda ki bayyanar da ko kadan daga cikin adonki wanda kika san in wani namijin ya gani zai ji dadin ganin ko ya yaba.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.
Matakan Tsaron Uwargida (2)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama…