✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mataimakin Abacha, Oladipo Diya ya rasu

An taɓa yanke masa hukuncin kisa sakamakon yunƙurin juyin mulki.

Laftanar Janar Oladipo Diya, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasar Najeriya zamanin mulkin Janar Sani Abacha ya rasu.

An taɓa yanke masa hukuncin kisa sakamakon yunƙurin juyin mulki amma kafin a zartar da hukuncin Abacha ya rasu.

Janar Oladipo Diya ya rasu ne a daren Lahadi a wani asibiti da ke Legas ya na da shekaru 78.

Babban ɗan marigayin, Oyesinmilola Diya ne ya sanar da rasuwar.

An dai haifi Oladipo Diya ne a garin Odogbolu da ke Jihar Ogun a ranar 3 ga Afrilu, 1944.

A zamanin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari ya zama gwamann Jihar Ogun daga Janairun 1984 zuwa Agustan 1985.

Daga nan ya zama Babban Hafsan sojin Najeriya kafin likkafa ta yi gaba ya zama mataimakin shugaban ƙasa Janar Sani Abacha.

Sai dai Janar Abacha ya tuhumi Janar Diya da yunƙurin yi masa juyin mulki.

Kuma kotun soji ta tabbatar masa da laifin har ta yanke masa hukuncin kisa, amma kafin zartar da hukuncin Allah Ya yi wa Janar Abacha rasuwa.

Gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar kuma ta sake shi.