✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mata zaman banza ba namu ne ba’

al’amurrana ba tare da na samu matsala ba, kuma da taimakon Allah komai na tafiya daidai. Ci gaban da na samu: Ci gaban da na…

al’amurrana ba tare da na samu matsala ba, kuma da taimakon Allah komai na tafiya daidai.

Ci gaban da na samu:
Ci gaban da na samu shi ne  tarbiyyantar da ’ya’yana ta hanyar da ta kamata , ba ma a Najeriya ba sun yi karatun digirinsu ne a kasashen waje. Mahaifinsu ya rasu ne a lokacin da ’yata ta fari take da shekara bakwaia duniya.  Kin ga ba don ina da abin yi ba, da duk wannan dawainiyar da na dauka ba za ta yiwu ba.  Kuma ba ’ya’yan kadai ba ’ya’yan wasu ma sun samu digirinsu ta dalilina.  Wasu a kasahen waje wasu kuma  a nan Najeriya, ba ’yan uwana ba kawai,   wadanda zaman tare ya hada mu, idan na ga ba su da karfi ina tallafa musu don  su yi ilimi su ma su nemi na kansu.  Idan  kowa zai yi haka na tabbata al’umma za ta gyaru.  Alal misali a ce kowa ya dauki nauyin  mutum daya wajen taimaka masa, shi ma wannan  ya taimaka wa wani, da haka har abin ya yadu kowa ya samu, da muna yin haka da ba za mu tsinci kanmu a halin da muke ciki ba a yanzu.

kalubalen da na fuskanta:
 A lokacin da na tsaya takarar  Majalisar Wakilai daga Jihar Adamawa, kin san mutanenmu da an gan ke mace ce, sai a shiga maganganu. Kuma na ga koma bayan ilimin mata da ’ya’yanmu, sai na ga cewa, kodayake ban  samu  nasara  ba, amma na sa mata  da yara da yawa a kungiyar Foreber suna  amfana  wurin tallafa wa rayuwarsu, ba abu ba ne mai  sauki.

Abin da na fi so:
A gaskiya noma, shi ya sa na bude gidan gona da ake kira KWADA FARMS.  Ana yin noma da kiwon kaji da sauransu.

Yadda nake so a tuna da ni:
Ina nan ina yin abubuwa da dama wadanda idan Allah Ya ba ni ikon kammala su to Insha Allahu mata musamman na Arewa ba za su manta da ni ba.

Shawarata ga matan Arewa:
A tashi tsaye a nemi abin yi , saboda mafi yawan abin da ke kawo mutuwar aure, ba komai ba ne illa talauci. Talauci  ne ke sa ma’aurata jin haushin juna da kuma rashin llimi. Ya zama dole mu nemi ilimi sannan mu nemi sana’a komai kankantarta a sannu da rokon Allah sai ta yi albarka. Zaman banza ba namu ba ne matan Arewa.