✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata xari sun samu tallafi kan lafiya a Katagum

Mata xari a masarautar Katagum sun samu tallafi kan kiwon lafiya. Alhaji Ghali Abdulhamid Ma’ajin Maxangala ne ya xauki nauyin biya wa matan kuxin magani zuwa…

Mata xari a masarautar Katagum sun samu tallafi kan kiwon lafiya.
 Alhaji Ghali Abdulhamid Ma’ajin Maxangala ne ya xauki nauyin biya wa matan kuxin magani zuwa tsawon wata 15.
Tallafin ya kama tun daga ganin likita da gwaje-gwaje da ba da gado da yin tiyata da kuma magunguna kyauta.
Da yake qaddamar da shirin nasa a garin Azare Alhaji Ghali ya ce wannan shirin na ba da tallafin magani ga mata xari a yankin masarautar Katagum tamkar biyan bashi ne sakamakon renonsa da tarbiya da kuma ilimin da masarautar ta ba shi.
Ya ce “Na yi niyyar yi wa mata 500 ne, amma sai  na tura wa sashin kula da kiwon lafiya na duniya don neman shawarar su da kuma amincewar su, sai suka ba ni shawara na fara gwaji a kan mata 100, idan an kwana biyu kuma sai na qara wasu mutane xari, daga nan har na kai ga adadin yadda nake so xin.”
A jawabin Alhaji Bukari Uba, Jami’i a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Azare, wanda shi ya jagoranci bikin qaddamar da shirin ya buqaci masu kuxi su yi koyi da irin wannan aiki na alheri.
Shi ma da yake jawabi Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Kiwon Lafiya da Magunguna ta Duniya da ke shiyyar Bauchi, Malam Khalid Qasimu ya ce: “A samu mutumin da ya tallafa wa mata xari tun daga ganin likita da gwaje-gwaje da ba su gado da yin tiyata da ba da magunguna kyauta abin a yaba ne.
Malama Iyallu Abdullahi Gaxau xaya daga cikin matan da za su amfana da wannan tallafi ta gode wa Alhaji Ghali. Ta ce: “Na daxe ina jinya amma ban tava samun tallafi ba sai a wannan karon. Ina yi wa wanda ya tallafa mana fatan alheri.”
Ita kuwa Malama A’isha Muhammad da ta daxe tana fama da ciwon hawan jini ta samu wannan tallafin inda ta ce a kullum ta je asibiti sai dai ta dawo da takardar sayan maganin gida, don kuwa a mafi yawan lokaci ba ta da halin saya. Don haka ta gode wa Alhaji Ghali da ya kawo mata wannan xauki.
Malam Hassana Ibrahim ta buqaci masu kuxi da su riqa tunawa da talakawa domin idan mutum yana da dukiya an ba shi damar da zai nemi aljanna da ita ne.