✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata a nemi ilimin aure kafin yinsa(3)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban rubutun da muke kawo muku:Amma idan manemin ba mutumin kirki ba ne, malamai…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban rubutun da muke kawo muku:
Amma idan manemin ba mutumin kirki ba ne, malamai sun yi bayanin ya halatta a wargaza shirinsa.  Idan namiji zai yi zance da mace, to a kiyaye wadannan sharudda:
(1)     Kada ku kebanta a wani wuri na daban, ya zama akwai wadansu a wurin, walau daga bangaren namiji ko mace, don kada a yi barna.
(2)    Kada ku yi wa juna kallon jin dadi ko sha’awa.
(3)    Kada ku yi musabiha ko ku taba jikin juna, hakan bai halarta ba har sai an daura aure.
(4)    Ya zama akwai kyakkyawar niyyar yin aure.
(5)    Ya halatta ku yi zance, ka tambaye ta, ta tambaye ka abin da ya dace, don ku fahimci juna, don kada a yi aure daga baya a zo ana da-na-sani.
(6)    Kada ku fita yawo ko shakatawa, ko da an sa ranar aure, yin hakan haramun ne ko da kuwa babu abin da zai faru, fita yawo ko shakatawa bai halarta ba, har sai an yi aure (Baiko fa ba aure ba ne tun da ana iya warware alkawarin saboda wani dalili, don haka sai a yi a hankali). Duba (‘Fikhus Sunnah Linnisa’i’ na Abu Malik da ‘Baiko Ba Aure Ba Ne’ na Mal. Ahmad Murtala Kano).
   Da za a kiyaye wadannan sharuddan da za a samu natsuwa da jin dadi; rashin kiyaye su ne ya haifar mana da abubuwan takaici da ‘ya’yan shegu marasa asali.
   Idan abubuwa sun daidaita, sai batun daura aure tare da kiyaye wadannan sharuddan:
(a)    Waliyyi: Dole ne a samu yardar waliyyi, don duk auren da aka daura ba tare da yardar waliyyi ba, to auren bai yi ba, idan akwai rikici ko matsala, sai shugaba ya shiga maganar ya warware ta, amma ta hanyar da ta dace.
 Duk matar da ta daura wa kanta aure ba tare da waliyyinta ba, ta zama karuwa domin: “Mazinaciya ce ke aurar da kanta.”
A nan nake jan hankalin iyaye su daina yi wa ‘ya’yansu auren dole, don hakan ba daidai ba ne, kuma hakan yana haifar da illoli masu yawan gaske,  Manzon Allah (SAW) yake cewa: “A nemi shawarinsu, a tambaye su, don a samu daidaito.” Don haka iyaye a bar yarinya ta auri wanda take so.
(b)    Sadaki: Dole ne a bayar sadaki a bisa abin da aka amince a kansa, mai sauki, wanda babu tsanani a ciki, don samun albarka a wurin Allah (SWT). Manzon Allah (SAW) ya ce: “Albarkar aure na daga karancin sadaki.” Allah (SWT) Ya ce: “Ku ba mata sadakinsu, kyauta ce (daga Allah, da dadin rai)” (Nisa’i 04).
  Don haka sadakin na mata ne, kuma idan babu matsi sai a bayar da yawa babu laifi, don sadakin Manzon Allah (SAW) yana da yawa. Amma batun dole kayan aure sai ya kai kaza ko sai an yi akwati adadi kaza, wannan ba ya cikin sharadin aure, da fatan iyaye da ‘yan mata za su hankalta.
   (C) kulla aure: Wasu kalmomi ne da ake amfani da su na nema da bayarwa, idan an yi wannan tsakanin waliyyin mace da miji ko wakilinsa, shi ke nan, aure ya kullu, sai a sanar da jama’a.
 Amma  zuwa wuraren barna na masha’a tare da maza da mata haramun ne, yahudanci ne, kuma hakan ne ke sanya aure ya mutu da tun ba a je ko’ina ba. Allah Ya sauwake.
  Bayan an gama wannan, sai mata masu hankali da natsuwa su dauki amarya su kai ta gidan mijinta, tare da yin nasihohi ko bayar da shawarwarin da suka dace, don tabbatar da zaman lafiya da samun arziki. Don karin bayani a duba (Fikhus Sunnah’ na Sayyid Sabik, da ‘Adabuz Zifaf’ na Albani).
Fadakarwa:     
(a)    Idan an daura aure, kafin matar ta tare a gidan mijinta, ko bayan ta tare, ana son a gabatar da walima. Walima sunnah ce mai karfi, a yi ta da abin da Allah (SWT) Ya hore, ko da taimakon da za a samu, a tara mutane maza ne ko mata bisa tsarin shari’a, a ci abinci, wannan shi ne walima. Mata na iya shirya walimarsu matukar babu sabon Allah a ciki, duba littafin ‘Azzawaj’ na Dk. Muh’d Ibrahim Alhafnawy 41).
  Manzon Allah (SAW) Ya yi walima, kuma ya kwadaitar da Sahabbansa (RA) su yi, har ma ya ce wa Anas bin Malik (RA) yayin da ya yi aure: “Ka yi walima ko da (yankan) dan akuya ne.” (Bukhari 5169).
   Kuma duk wanda aka kira shi dole ne ya amsa, sai dai idan yana da uzuri, sai ya sanar, kuma duk wanda ba a kira shi ba, idan ya je, ya yi laifi.
(b)    Taya ma’aurata murna da farin ciki sunna ce, tare da yi musu addu’a, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake yi:  “Barakal lahu laka, wa baraka alaika, wa jama’a baina kuma fi khairin”
Ma’ana: “ALLAH YA YI MAKA ALBARKA, YA kARA MAKA ALBARKA, YA HAdA KU CIKIN ALKHAIRI”  (Abu Duwud, Tirmizy da Ibnu Majah. Hadisin Abu Huraira).
   Ana iya bayar da gudunmawa gwargwadon hali idan akwai, kamar yadda Hadisai da dama suka tabbatar da taimakekeniya a tsakanin Sahabbai (RA), amma a debo rikicin aure don gadarar gudunmawa da roko ko maula ba daidai ba ne.
  (C) Yayin da ango zai shigo bayan an kawo masa amarya dakinta, ana son ya yi sallama, wannan alama ce ko albishir ne na samun SALAMA (zaman lafiya) a tsakani Insha Allahu, domin bayan Ummu Salma (RA) ta tare gidan Annabi (SAW), da zai shigo, sai ya yi mata sallama. Yana da kyau, ya shiga da wani abin dadi ko zaki, sai ya fara kurba sannan ya ba ta, ita ma ta sha, saboda haka Annabi (SAW) ya yi, yayin da ya shigo dakin Nana A’isha (RA) (Hadisin Nana Asma’u (RA), Riwayar Ahmad 6/456), kuma muhimmin abu ne su tashi su yi alwala don su yi sallar nafila raka’a biyu tare, idan ba ta cikin jinin al’ada, yana gaba, amarya na baya, bayan sun kammala kuma sai su yi addu’a, zai yi addu’ar Allah Ya ba shi alherin matar, ya kuma nemi tsari daga sharrinta, kamar yadda Abdullahi bin Mas’ud, Abu Zarr da Huzaifah (RA), suka bayyana wa Abu Sa’id Maulan Abu Asid (Riwayar Ibnu Abi Shaibai).
  Akwai wata addu’ar da take da muhimmanci ainun, sai ya riki gashin goshinta, ya yi Bismillah, sai ya ce:
   “ALLAHUMMA INNI AS’ALUKA MIN KHAIRIHA, WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAIH, WA A’UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIH.”
Ma’ana: “Ya Allah lallai ni ina rokon Ka alherinta (wannan amaryar) da alkhairin da Ka halicce ta a kansa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrinta, da sharrin da Ka halicce ta da shi.” (Abu Dawud 2160, Nasa’i 241-264 da Ibnu Majah 1981).