✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata a nemi ilimin aure kafin yinsa(2)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba mukalar da muka fara kawo muku a makon da ya gabata:Fa’idojin aure  Idan…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba mukalar da muka fara kawo muku a makon da ya gabata:
Fa’idojin aure
 Idan kuka yi aure to za ku wayi gari kun cimma wasu  abubuwa da dama, ga kadan daga ciki:
•     Kun yi biyayya ga umurnin Allah (SWT) kamar yadda ayoyi suka gabata.
•    Kun bi sunnar Manzon Allah (SAW); sun yi koyi da shi, kuma za su samu natsuwa da kwanciyar hankali.
•    Kun yi maganin sha’awarsu ta ‘yan Adam, sun kuma kare mutuncinsu.
•    Kun biya bukatarsu ta hanyar da ta dace, ba ta tsinanniyar hanya ba!
•    Kun taimaka wajen magance yaduwar barnace-barnace da ayyukan ash-sha.
•    Kun kara yawan al’ummar Manzon Allah (SAW), idan kun hayayyafa kamar yadda Annabi (SAW) ya ce: “Lallai idan kun yi aure kun hayayyafa, zan yi takama ga sauran al’umma” (Abu Dawud 2050, Nasa’i 6/75).
•    Ga samun lada mai yawa a wurin Allah, domin ladan aure kamar na sadaka ne, don Annabi (SAW) ya ce: “a cikin jima’in dayanku ma akwai (ladan) sadaka” (Muslim 1006, Abu Dawud 1286).
Siffofin wanda ake aure
Akwai  siffofi da ake so, maza da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin su nemi junansu da aure, don samar da farin ciki da natsuwa a tsakaninsu, ga su nan kamar haka:
Siffofin miji
A duk lokacin da mace ta tashi aure to yana da kyau ta fahimci shin mijin da za ta aura ya mallaki wadannan halayen:
 –  Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, don mai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.
–    Ya kasance ya haddace wadansu ayoyin Alkur’ani, don sukan kara wa bawa imani, wanda ya haddace ayoyin kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne a wurin Allah.
 – Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, zagi, takuri da cin mutunci ba, a inda babu gaira babu dalili.
–    Ga miji kuma ya kasance yana da kuzarin biyan bukatar iyalinsa da nemo wa matarsa abinci, sutura, wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum tun da Annabi (SAW) ya ce:  “Wanda yake da hali daga cikinku ya yi aure…” (Bukhari 5065, Muslim 1400).
–    Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, da samun zamantakewa mai kyau.
–    Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakan ne ta hanyar ‘yan uwansa ko zuriyarsa. Kodayake haihuwa ta Allah ce, Yakan ba wani, ya kuma hana wani.
–    Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtar juna, don samun zaman lafiya. A nan nake jan hankalin ‘yan uwa mata da kada su kuskura su auri mutumin banza, don za su shiga mayuwacin halin da zai sa ba za su ji dadin rayuwarsu ba har abada! Duba (Sahih Fikhis Sunnah 3/103-107).
Siffofin matar da za a aura    
Ana so mata su kasance:
•    Ma’abota addini. Manzon Allah (SAW) ya ce:  “…ka rabauta da mai addini, za ka yi riba.” (Bukhari 5090, Muslim 1466).
•    Masu kyau, hali da mutunci, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya fara lissafawa a hadisin da muka ambata a sama.
•    Masu tausayi da kauna, wanda ba za su azabtar da miji ko wulakanta shi ba, don Annabi (SAW) ya ce:  “Wadannan su ne mafiya alherin mata.”
•    Masu amana da biyayya, Manzon Allah (SAW) ya yaba wa irin wadannan matan, amma mace fitsararriya ko shedaniya babu abin da za a samu daga gare ta sai fitina da tashin hankali.
•    Budurwa, su kasance wani bai taba saninsu ba, don akwai wanda ya yi aure a zamanin Manzon Allah (SAW) sai ya tambaye shi, “Budurwa ce ko bazawara?” sai ango ya amsa da cewa: Ai bazawara ce, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “ai da budurwa ce (ka aura), ka yi wasa da ita, ita ma ta yi wasa da kai!” (Bukhari 5079, Muslim 715). Ba wai an hana auren bazawara ba ne, matukar an samu fahimta, sai dai ba a san abin da ya rabo ta daga gidan mijin farko ba, don haka a yi kokarin kiyaye martabar aure, idan an yi sakin nan ba alheri ba ne, idan babu dalili.
•    Masu haihuwa, saboda Hadisin da ya gabata a can baya na yawaitar al’ummar Manzon Allah (SAW) da yin aure, ga wanda Allah (SWT) ya kaddara musu haihuwa.
 Wadannan siffofi ake bukata ga ma’aurata su siffantu da su, don tabbatar da alherin aure da samar da natsuwa da kwanciyar hankali duniya da lahira. Allah Ya azurta mu da mata nagari haka su ma matan ya ba su mazaje na gari.
 Neman aure da kulla shi:
 Idan namiji yana son wata, kuma yana son ta da aure, to ya halatta ya kalle ta yadda ya dace, don tabbatar da abin da ya yi niyya, idan Allah (SWT) Ya yarda.
   Wannan gani da zai yi mata, Musulunci ya halatta masa, tun da gani ne na neman tabbatar da alheri ba na barna ba, bayan samun izinin waliyyanta, bayan ya gan ta, sun zanta sun amince da juna, to haramun ne kuma wani ya yi kundumbala ya shigo, saboda fadin Manzon Allah (SAW): “Kada wani ya yi neman aure a kan neman dan uwansa, har sai ya bari (idan ba a samu amincewa ba), ko kuma sai mai neman ya ba shi izini (idan ya ga kamar ba zai kai labari ba)” (Nasa’i 6/73 don karin bayani duba littafin Alwajiz 281-282).