✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 100 masu yoyon fitsari sun koyi sana’a a Katsina

An yi bikin yaye dalibai mata masu ciwon yoyon fitsari su 100, bayan sun kammala koyon sana’o’in hannu da suka hada da dinki da saka…

Wadansu daga cikin irin kayayyakin da aka ba suAn yi bikin yaye dalibai mata masu ciwon yoyon fitsari su 100, bayan sun kammala koyon sana’o’in hannu da suka hada da dinki da saka da rini da sauransu da aka gudanar a karkashin Cibiyar Harkokin Mata da ke kusa da asibitin Babbar Ruga a yankin karamar Hukumar batagarawa.
Su wadannan daliban, wadanda su ne kashi na 4 da cibiyar ta yaye, suna daga cikin mata masu ciwon yoyon fitsarin da suke jiyya a asibitin ta Babbar Ruga.
Cibiyar ta bullo da wannan shirin ne da nufin tallafa wa matan tare da kara musu kwarin gwiwa ta samun sana’ar yi a yayin da suka koma ga iyalansu, musamman dayake har ana koya musu karatu da rubutu.
Uwargidan gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Shema, wadda a matsayinta na uwa kuma babbar bakuwa, ta bukaci wadanda aka yaye din su rungumi sana’o’in da suka koya da hannu bibbiyu kuma su shiga harkokin kasuwanci gadan-gadan da kuma harkokin noma, tunda an koya musu irin su kiwon kifi da noman zogale da kayan miya da sauransu, ta yadda za su dogara da kansu.
Uwargidan ta yi kira ga maza da su rika tallafa wa irin wadannan mata ta duk wata hanyar da ta dace bisa la’akari da matsayinsu. Sannan ta yi kiran da a cigaba da yin addu’o’in neman ceto ’yan matan Chibok tare da samun zaman lafiya a Arewa da kasa baki daya.
Tun farko a jawabinta, Kwamishinar harkokin mata ta jihar, Hajiya Amina Isa Gachi ta yaba wa gwamnati kan gudunmuwar da take bayarwa ta wannan fuska tare da sashen kudurorin Cimma Muradun karni (MDG) a cikin tsawon watanni tara (9) da aka dauka ana koyar da su.
Hajiya Amina ta ce, wannan sashe na MDG, ya rika ba kowace daliba Naira dubu bakwai a kowane wata, sannan kuma ga wata Naira milyan biyar da sashen ya bayar da aka raba wa matan. A kan haka sai kwamishinar ta yi kira gare su da su tabbata sun yi amfani da wannan tallafi da kuma kayayyakin da za aka ba su ta hanyar da ta dace.
Su ma ana su bangaren, matan da abin ya shafa sun nuna matukar farin cikinsu ta bakin shugabarsu, Malama Magajiya Ahmed, wadda ta ce gaskiya zamansu a asibitin sun samu canjin rayuwar da ba su taba tunaninta ba. “Mun koyi tsafta da yadda za mu zauna a tsakanin jama’a, sai kuma ga wani babban al’amari na yadda za mu dogara da kanmu ta fuskar koyon sana’o’i. Muna godiya ga dukkan wadannan suka taimaka mana”, inji ta.
Su dai wadannan mata 100, sun fito ne daga jihohin Adamawa da Borno da Binuwe da Bauchi da Kaduna da Kano da Katsina, wadda ke da dalibai 56. Sai kuma Nasarawa da Neja da Sakkwato da Yobe da Zamfara. Haka nan sun hada da mata 8 da suka fito daga Jamhuriyar Nijar.
Kayayyakin da aka raba musu sun hada da injunan markade da na saka da kekunan dinki da kuma katifu 100 hade da matasan kansu, wadanda uwargidan gwamna, Hajiya Fatima Shema ta ba su, a matsayin tata gudunmuwar.
Shi ma gwamnan jihar ta Katsina, Barista Ibrahim Shema ya dauke wa kowace mace kudin motar da zai kai ta gida tare da kayanta don saduwa da sauran ’yan uwa, a matsayin tashi gudunmuwar.