Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci masu tattakin zuwa Kano daga wasu jihohin kasar nan don taya shi murnar lashe zabe da su daina.
A maimakon haka, ya roke su da su yi masa addu’a don samun basirar yin jagoranci wajen ganin ya samar da ribar dimokuradiyya.
- Majalisa za ta binciki musabbabin yawan hatsarin jirgin kasa a Najeriya
- DAGA LARABA: Matakan Samun Nasara A Watan Ramadan
Wasu kafafen sada zumunta sun rawaito cewa tuni wani matashi da wasu daban suka fara tattaki daga Suleja a Jihar Neja domin taya sabon Gwamnan na Kano mai jiran gado murna.
Sai dai Abba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce addu’o’i sun isa a matsayin nuna goyon baya da kuma murnar nasarar da ya samu a zaben ranar Asabar, kuma ba tafiya mai nisa da wasu masu kishinsa suke yi ba, musamman duba da halin rashin tsaro da kasar ke fama da shi.
Ya ce, “Yayin da yake mika godiyarsa ga magoya bayansa a ciki da wajen Jihar Kano, zababben gwamnan, ya bukaci masu tattakin da su daina domin hakan ba zai taimaka ba wajen magance dumbin kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da ke jiran gwamnati mai jiran gado bayan ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023 ba.
“Gwamnatin Jihar Kano mai jiran gado za ta himmatu wajen samar wa al’umma ci gaba ta fuskar tsaro, kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kyautata jin dadin ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu su ne burin Injiya Abba.”
Abba ya bukaci a hada karfi da karfe don ganin an samar da ci gaba da kuma tabbatar da muradan Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.