Masu kiwon kaji da ’yan kasuwa na kokawa da halin da suka tsinci kansu a Karamar Sallar bana a jihar Kano saboda rashin ciniki da kuma yanayin kajin saboda yanayin zafi da matsin tattalin arziki da ake ciki.
A duk shekara Musulmai da dama a Najeriya da sauran duniya na yin abincin karamar Sallah da naman kaji, zabi da sauran dangin tsuntsaye na gida.
Haka kuma akwai masu kiwon tsuntsayen domin kasuwanci ko domin sanya su a abincin Sallah.
Masu kiwo ko kasuwancin kaji na samun alheri saboda yanayin bukatar kajin da al’umma suke da ita a irin wannan lokaci.
A kan haka ne Aminiya ta yi duba ga halin da ake ciki inda da ziyarci kasuwannin Kano inda ga gana masu kiwo da hada-hadar kaji domin sanin yadda take kayawa a Karamar Sallar bana.
Yanayin zafi ya jawo mana asara —Masu kiwo
Adamu Hamza wanda ke kiwon kaji sama da dubu daya a wani matsakaicin gidan gona, ya koka kan yadda tsakanin zafi ya sanya akasarin kajinsa mutuwa ko galabaita.
“A gaskiya bana sai godiya kawai. Yanayin zafi ya zo mana da canji a wannan harka tamu.
“Idan ka duba, za ka ga kajin ba su yi kyau yadda ake tsammani ba saboda zafi na damun su suma. Sakamakon haka ba sa iya cin abinci yadda ya kamata.
“Ni yanzu addu’a nake kudin da na kashe su dawo, ba ma batun riba ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Guda dubu daya da dari biyu na zuba amma abin da suka tsira ba su wuce dari bakwai ba. Ka ga kuwa sai hamdala kawai.”
“Gashi Sallar ta zo amma kamar ba Sallah ba. Yadda ake neman kajin ba kamar a shekarun baya ba.
“A shekarar da ta gabata, a lokaci irin yanzu kajin sun ma kare kuma ana nema.
Shi kuma Sunusi Muhammad, cewa ya yi yanayin kasuwar ta kaji a bana sai hakuri.
“Ni da na saba sayar da kaji na gaba daya a lokaci guda, yanzu idan masu dauka suka zo maka sai su ce zaba za su yi saboda kajin zafi ya hana su girman da ya kamata.”
Ya ce duk da haka, masu sarin kajin, “Idan sun zaba, korafi suke kajin sun musu yawa kuma ba fita ake yi ba. Babu masu saya kamar shekarun baya.”
“Lissafi mu muke yi tun daga ranar da muka zuba su zuwa ranar da za su fita.
“Idan kaza ta kara kwana daya a hannunka, to ta zama jagwal — Za ta koma cin abinci ne a cikin ribarka.
“A haka ba na maka lissafi da wadanda kawai na yanka su saboda gudun asara da kuma wadanda suka mutu. Sai hakuri da fatan alheri kawai. Haka kasuwa takan juya dama.
’Yan kasuwa na cigaba da zaman tsammani
A wani kewaye da Aminiya ta yi a wurin ’yan kaji a kasuwar Tarauni, wadda ta yi suna wajen hada-hadar kaji, Sunusi Danbaba, ya alakanta halin da ake ciki da rashin kudi a hannun jama’a.
“Gaskiya hada-hadar kaji ga ta nan, babu cash a hannun mutane, sai a hankali gaskiya.
“A na dan saya, biyar goma… amma muna kwantan kai da kafa saboda babu ciniki.
“Ba za ka hada shi da shekarar da ta gabata ba — Waccan an fi ciniki.
“Kazar N2,200 ta dawo N2,000, har N1,800 ma za mu iya sayar maka. Kilo daya muna sayar da shi dubu daya da dari biyu.”
Nuhu Mai kaji, Unguwar Kubuta, Dansarai, Kan Titin Hadejia ya ce, “Da mukan sayar da zabo dubu uku da dari biyu zuwa da dari biyar; Yanzu ya kai dubu uku da dari takwas zuwa dubu hudu.
“A wannan masana’anta tamu da ke Gunduwawa, abin da ya lawo karin, Sallah ce. Kowa dole yana kokari ya saya gwargwadon yadda Allah Ya hore masa.
“Mun fi ciniki a bara saboda akwai kudi a hannun jama’a amma yanzu babu.
“Da bara kuka zo nan lallai za ku shaida cewa lallai Sallah ta zo. Amma yanzu duk kun tadda mu a zaune kamar almajirai muna jiran tsammani muna ta addu’a.”
“Duk wanda ya san yadda kaji suka zama a shekaru biyu baya, zai tausaya mana a bana domin an samu canji matuka.
“Shekaru biyu baya a ranaku irin yanzu da ya rage Sallah saura kwanaki kalilan, ai kajin ma wahala suke,” cewar mani mai sayar da kaji, Abdulmajid Ya’u.
Duba ga girman bukatar kaji a lokacin Sallah, me ya sa harkar ba ta tafiya duk da wadannan dalilai masu karfi?
Wani dattijo, Musa Abdullahi ya alakanta yanayin da rashin kudi a hannun jama’a.
“Halin da ake ciki ina ruwan wani da kaza a wannan yanayi, ai ta abin da za a ci a koshi ake yi yanzu. Duk wanda ka ga ya sayi kaza ai ya koshi ne.
“To kuma akwai al’ada, an saba duk lokaci irin wannan da dadi ko babu dadi za ka ga ana kokarin sayen kajin ko yaya dai domin a faranta wa juna da kuma yara. Allah dai Ya iya mana.”