✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu ruwa-da-tsaki sun yaba wa CBN kan hana musayar kudaden waje ga kayayyaki 42

Babban Bankin Najeriya na CBN ya bullo da ka’ida wacce ta togace bai wa masu shigo da kayayyaki kamar tufafi da tsinken sakace hakori da…

Babban Bankin Najeriya na CBN ya bullo da ka’ida wacce ta togace bai wa masu shigo da kayayyaki kamar tufafi da tsinken sakace hakori da shinkafa da makamantansu samun musayar kudaden kasashen waje. Masu ruwa da tsaki sun ce dokar ta taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasa.

Yayin shigarsa ofis a watan Yunin shekarar 2014, Gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele a jawabinsa na amincewa da nadin da aka yi masa ya bayyana cewa daya daga cikin abin da yake son cimmwaa a matsayinsa na Gwamnan Bankin CBN shi ne mayar da hankali kan bunkasa bankin da zai fuskanci gina tsarin kudi mai karfi da zai ceto tare da bunkasa da ci gaban kasar nan.

Sai kuma mayar da hankali kan tattalin arziki kamar daidaita farashin kayayyaki da daidaita darajar Naira. Mista Emefiele ya tabbatar da ganin cewa Bankin CBN ya taka rawa wajen tallafa wa tattalin arzikin Najeriya musamman ta bangaren noma da masana’antu bisa la’akari da matsalolin da manoman karkara suke fuskanta da kananan ’yan kasuwa da kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki.

Ya bayyana cewa kimanin shekara biyar da suka gabata dalillan da suka sanya daukar wannan mataki shi ne imanin da aka yi na magance kalubalen ci gaba ba wai kawai za su karfafa ci gaban tattalin arziki ba ne har ma zai kai ga samar da guraben ayyukan ga al’umma.

“Sakamakon matakan da Bankin CBN ya dauka wadanda suka hada da tsaurara dokokin kudi da ya fara daga shekarar 2016 da kafa tsarin masu zuba jari da masu fitar da kaya a watan Afrilun shekarar 2017 da hana bayar da musayar kudin kasashen waje ga kayayyaki 42 da za a iya sarrafawa a gida da bunkasa shirin bayar da tallafi don tallafa  noman wasu kayayyakin abinci kamar shinkafa da tumatir da kifi sun taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya,” inji shi.

Da yake bayar da kididdiga ya ce “Bankin CBN ya samu ragin kudin da yake kashewa wajen tallafin shigo da kayan abinci a wata wanda ya ragu daga Dala miliyan 665.4  a watan Janairun shekarar 2015 zuwa Dala miliyan 160.4  a watan Oktoban shekarar 2018 wanda gaba daya ya fadi zuwa kashi 75.9  cikin kashi 100 inda aka samu ajiyar fiye da Dala biliyan 21 kan shigo da kayan abinci kawai a wannan lokaci.”

“An samu ci gaba mai yawa amma ana bukatar a kara kokari don tabbatar da mun gina tattalin arziki na bai-daya wanda zai tallafa wa samar da kayayyaki a gida tare da samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Najeriya” inji shi.

Gwamnan CBN ya bayyana cewa wannan shi ne mafita tilo da muke da ita idan muna son kare tattalin arzikinmu daga dogaro a kan man fetur wanda ba ya da tabbas a kasuwar duniya.

Don cimma burin da ake son cimmawa, Bankin CBN da masu ruwa-da-tsaki suka gano wasu kayayyaki kamar tufafi da manja wadanda za su iya samar da daruruwa da dubban guraben ayyukan yi a tattalin arzikinmu.

Da yake sharhi kan wannam mataki, Shugaban Hukumar Jiragen Ruwa ta Najeriya, Barista Hasan Bello ya ce cibiyar tana goyon bayan matakin Bankin CBN.

“Ba ta yadda za a yi mu ci gaba da kasancewa masu dogara da kayayyakin da ake shigowa da su kasar nan. Yayin da kwantainoni suke ta sauka a nan suna ci gaba da barinmu fanko hakan yana shafar kudin sufuri. Dokar Bankin CBN ta samar da karuwar fitar da kayayyakin da ba man fetur ba a karon farko. Hakan shaida ce ga raba kafar da aka yi na tattalin arziki da karfin gwiwar da muke da shi a kan tattalin arzikinmu,” inji shi.

“Dakatar da bayar da musayar kudin kasashen waje kan tufafi da sauran kayayyaki ba wai nuna wariya ba ne sai dai bayar da dama ce ta bai-daya ga masu sarrafa kayayyakinmu a nan gida saboda mafi yawan kayayyakin sutura misali fasakwaurinsu ake yi zuwa Najeriya. Muna da masaku  kimanin 15 da suke daukar dubban daruruwan ma’aikata. Kamar bangaren karafa ne ko kuma kamfanonin kayayyakin sufuri a kasar Amurka. Saboda yadda dokokin Amurka suke tallafa wa kamfanoninsu na gida akwai ka’idoji masu tsauri dangane da shigo da karafa Amurka,” inji shi.

Ya bayyana cewa karancin masaku a Najeriya ya shafi kasar kwarai da gaske. “Masaku tamkar wata sarka ce kuma dukan sassan sarkar an lalata su. A yanzu muna sanyo tufafi daga kasashen waje. Dokar ba wai kawai tana takaita gasa ba ne har ma da bai wa masu masana’antunmu na gida dama. Ya zama wajibi mu yaba wa Bankin CBN kan wannan tunani,” inji shi.

Da yake sharhi, masanin tattalin arziki da kuma kasuwar hannun jari, Farfesa Uche Uwaleke wanda shi ne Shugaban Sashen Banki da Hada-Hadar Kudi a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi ya ce nan da zuwa wani lokaci farashin wasu kayayyakin da aka togace musamman sutura zai daidaita  kuma Najeriya za ta cimma buri kan sarrafa tufafi.

“Zai rage almubazzaranci ko kuma masakun ba za su ci gaba ba.” Ya ce dakatar da bayar da musayar kudaden kasashen waje da aka yi a baya kan kayayyaki 42 kwalliya ta biya kudin sabulu musamman da aka fadada shi.

“Ina zaton hakan saboda nasarar da aka samu ta hana bayar da musayar kudaden kasashen waje kan kayayyaki 41. Ka dubi darasin da aka samu kan shinkafa. Hatta tsinken sakace muna yin sa a nan gida Najeriya” inji shi.

“Idan Bankin CBN ya samu nasara kan hana bayar da musayar kudaden waje kan wasu kayayyaki kuma suka kara wasu kayayyaki. Hakan wata shaida ce ta cewa hanin yana aiki” inji shi.

“Nan da wani lokaci za mu cimma nasarar dogaro da kanmu kan tufafi mu samar da ayyukan yi. Hakan zai bunkasa tattalin arziki da kuma ci gabansa,” inji shi.

Da yake sharhi kan hana bayar da musayar kudaden waje kan tufafin da ake shigowa da su, Mista Anibe Achimugu, Shugaban Kungiyar Masu Noman Auduga ta (NACOTAN) ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa duk wani abu da za a yi don tallafa wa bangaren masaku yana da muhimmanci. Ya kara da cewa a matsayinmu na kasa ya zama wajibi mu hada hannu don tabbatar da samar da masaku masu inganci da a baya aka taba farfado da su. Gaskiyar ita ce idan ina samun musayar kudaden waje don shigo da tsofaffin tufafi ban ga yadda hakan zai taimaka wa masakunmu na gida ba. Saboda haka dokar da Bankin CBN ya bayyana wani abin yabawa ne. Hakan ya nuna da gaske Gwamnatin Tarayya take yi dangane da kokarinta na farfado da masakunmu na Najeriya,” inji shi.

Da yake karin bayani kan ko dokar za ta sanya tsadar tufafi, Mista Achimugu ya ce “Ba na tunanin wannan zai zama matsala. Idan ka tuna kasar Rasha an sanya mata takunkumi da ya ware ta daga hada-hada da kasashen duniya sai suka fara bunkasa masana’antunsu na gida don samar da abin da suke bukata. Idan ka kalli kasar Iran duk da takunkumin da aka sanya mata za ka yi mamakin abin da take yi da masana’antunta na masakunta da sauran bangarori. Dokar za ta sa mu farka mu nemo mafita don biyan bukatunmu.”

Ya ce masakun kasar nan suna da karfin biyan bukatunmu ya ce ya zama wajibi ’yan Najeriya su zama masu kishin kasa kuma su rika amfani da kayayyakin da aka sarrafa a Najeriya don samar da ayyukan yi.

Akwai abubuwa da dama dangane da amfani da tsofaffin tufafi. Ba ka san yadda aka samo su ba ko lafiyarsu amma idan ka sayi sabon kaya ka san inda aka samo shi, tsadar kayan bai kamata ta zama wata abar damuwa ba don alfanun zai bayyana a nan gaba kadan.

Dangane da auduga kuma Achimugu ya ce Najeriya “Tana da karfin samar da tan dubu 650 na auduga amma a yanzu ba ta samar da tan dubu 100. Muna da kamfanonin sarrafa auduga guda 52 a da, kamfanonin suna nan amma ba mu da ishasshiyar audugar da za mu ba su shi ya sa aka rufe su,” inji shi.  Ya kara da cewa idan Najeriya tana samar da tan dubu 650 a shekara manoma da yawa za su kara yawan noman da suke yi kuma za a samu kamfanonin sarrafa audugar masu yawa.

“Muna da karfin yi amma ya zama wajibi mu koma daga tushe. Muhimmin abin dogaron masaku shi ne auduga. Muna bukatar manomanmu su koma noman auduga muna bukatar tallafa musu don samar da ingantacciyar auduga wacce za ta dace ga dukan kayayyakin da masakun Najeriya suke bukata, amma inda suka kasa yana da sauki a shigo da injinan Najeriya don sarrafa su,” inji shi.