✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu haihuwa

Wasu mutane ne su uku, suka kai matansa asibiti domin haihuwa, daya ma’aikacin kamfanin 2 Effects ne, daya ma’aikacin kamfanin 3 Crowns, daya kuma ma’aikacin…

Wasu mutane ne su uku, suka kai matansa asibiti domin haihuwa, daya ma’aikacin kamfanin 2 Effects ne, daya ma’aikacin kamfanin 3 Crowns, daya kuma ma’aikacin kamfani 7Up ne. Suna zaune suna hira, suna jiran sakamakon matansu sai ga nas ta fito, ta ce: “Ina ma’aikacin 2 Effects?” Da ya ce ga shi sai ta ce masa: “An samu ’yan biyu.” Ya kama murna. Bayan ta shiga ta sake dawowa, ta ce: “Ina ma’aikacin 3 Crowns?” Ta ce masa: “An samu ’yan uku.” Da ta koma ciki, bayan kimanin miti biyar sai ta dawo, ta ce: “Ina ma’aikacin 7Up?” Sai ya kama kuka, yana tsammanin ’ya’ya bakwai matarsa ta haifa, ya ce: “Wayyo Allah, ga ni!” Sai ta ce masa: “An samu da daya amma ya koma.” Nan take sai ya ce: “Alhamdu lillahi!”
Daga Azzubair M. Fagge, 08034412272