✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun aika min wasika- Dan Majalisar Kaduna

Mataimakin shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Kaduna Shehu Yunusa Pambeguwa, ya bayyana yadda masu satar mutane suka aiko masa da wasikar barazana. Ya…

Mataimakin shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Kaduna Shehu Yunusa Pambeguwa, ya bayyana yadda masu satar mutane suka aiko masa da wasikar barazana.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da Kwamishinan tsaro da Al’amuran cikin gida Samuel Aruwan, ya bayyana a gaban Majalisar domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa a ranar Litinin.

Dan Majalisar ya kara da cewa, babu isashshen tsaro a Majalisar haka kuma a gidajensu wanda hakan ke bai wa ‘yan bangar siyasa damar zuwa ofisoshinsu suna yi masu barazana.

“Babu tsaro a nan majalisa haka kuma a gidajen mu domin ni ka‎ina nan sai da aka aiko min da wasika daga masu garkuwa da mutane da sauran su. Har takai na nemi a bani ’Yan Sanda domin kare gidana saboda anan iyalina suke,” in ji shi.