✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga na neman fansar N270m kan daliban ABU

’Yan bindigar na neman miliyan N30 a kan kowane dalibi a matsayin kudin fansa

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai tara na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun bukaci miliyan N270 a matsayin kudin fansa.

An sace daliban wadanda ke karatun harshen Faransanci ne a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a makon jiya.

Daya daga cikin wadanda suke motar lokacin da lamarin ya faru wanda kuma ya samu nasarar tserewa mai suna Dickson Oko ya shaida wa wakilinmu cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan daliban suna bukatar a ba su N30m a kan kowannensu.

Dickson, wanda ya tsira da tabban harbin bindiga ya ce yanzu haka yana murmurewa, ko da yake ya yi matukar kaduwa da sace abokan nasa.

Ya shaida wa Aminiya cewa yana daga cikin wadanda suka samu nasarar tserewa daga motar duk da harbe-harben da aka yi masa inda ya gudu ya bar wayarsa da jakarsa a ciki.

Sai dai ya ce lokacin da ya dawo wajen motar bayan harin, wayarsa da ma na sauran mutane duk an yi awon gaba da su.

Dickson da direban motar Nuruddeen Mohammed sun ce su 12 ne a cikinta kuma mutum tara aka dauke daga ciki.

’Yar uwar daya daga cikin wadanda aka sacen, ta shaida wa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa masu garkuwar sun kira iyalan daliban suna bukatar a biya N30m domin fansar kowannensu.

Ta roke su da su dubi Allah su sako su, tana mai cewa ’yan makaranta ne kawai kuma iyayensu talakawa ne.