✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun sako Shugaban UBEC da ‘yarsa

Shugaban UBEC da Dokta Mohammed Mahmood Abubakar da aka sace tare da ’yarsa jiya Yasmin a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya kubuta ya kubuta. Idan…

Shugaban UBEC da Dokta Mohammed Mahmood Abubakar da aka sace tare da ’yarsa jiya Yasmin a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya kubuta ya kubuta.

Idan ba a manta ba, a wata tattaunawa da Shugaban UBEC ya yi da wani dan uwansa da muka ruwaito dazun, an jiyo shi yana cewa duk inda za a nemo kudin, a je a nemo domin a biya kudin fansansa da ’yarsa da aka yi garkuwa das u jiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A cewarsa, “Don Allah ku hanzarta. Lokaci na kurewa. Idan aka yi magana ka ga zai dauki wani dan lokaci kafin inda za a yi mhada a karba, kuma wannan abu ne in Allah ya yarda ana so a gama cikin awa guda. Don Allah su tartara duk abin da za su tattara cikin awa daya.”

“Amma wanda aka ce an samu daga Abuja, na san zai yi wuya a kai kudi daga Abuja zuwa Kaduna a daren nan. Ga 30 (miliyan ken an yake nufi) a kasa, ga 13 yanzu ya zama 43 ke nan. Suran 17. Don girman Allah duk inda za a samu a nemo.”