✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu dakon fetur na nuna son rai wajen shiga yajin aiki

Edita, ina so ka ba ni fili a cikin jaridar Aminiya don na yi tsokaci a kan yadda kungiyar masu dakon fetur ta kasa NUPENG…

Edita, ina so ka ba ni fili a cikin jaridar Aminiya don na yi tsokaci a kan yadda kungiyar masu dakon fetur ta kasa NUPENG da takwarorinsu ke yawan shiga yajin aiki a kan matsalar da ta shafe su kawai ba ta daukacin al’umma ba.
A gaskiya abin da suke yi sam bai dace ba kuma su sani suna cutar da jama’ar kasa ne akan abin da ba su ji ba, ba su kuma ga ni ba.
Ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin sayo tankokin dakon fetur da kuma gida gidajen sayar da fetur fiye da na kungiyar masu dakon feteur a fadin kasar nan.  Yin haka zai sa su rika shiga taitayinsu wajen yin yajin aiki.
Daga Muhammad Sani Shokin
Sardaunan Matasan Tudun Wada Kaduna
08028797882

Sakonnin waya

Haba Hajiya Naja’atu!
Assalam alaikum. Aminiya, Hajiya Naja’atu kin manta lokacin da kike cewa Baba Buhari ba siyasar cin zabe yake yi ba? Da ke da su Goodluck din duk jirgi da ya kwaso su. Daga Isa Muhamamd Gabashi Ringim Giwa, Kaduna 08025744650.

Ta’aziyya ga masarautar Daura
Ina mika sakon ta’aziya ta ga al’ummar Daura da Masarautar Daura. Abisa rasuwar Sarkin Tarishi Alhaji Mamman Siya Abubakar. Da fatan Allah ya jikansa. Daga: Hassan Muhammad Binanchi, Daga Unguwar Magajin Garin Sokoto, 07032512064.

Dokat ta-baci
Allah Sarki dama Matsalar Gwannatin Najeriya Ke nan ana Gabas tana Yamma Kwannan baya Mun ji Gwannatin Najeriya ta Kafa Kwamitin Sasantawa da ’Yan kungiyar Boko Haram, sai kuma ga shi Gwannatin Najeriya ta Sanya Dokar ta baci a Jahohin Barno da Yobe dakuma Adamawa, mu dai fatarmu ita ce Allah Ya sa kada Sojojin Najeriya Su maida Rayuwar Al’ummar Najeriya, tamkar Rayuwar Naman Daji, saboda a halin Yanzu Sojojin Najeriya Sun fi ’Yan Sanda bakin Jini ga idanun Al’ummar Najeriya. Daga karshe fatarmu ita ce Allah Ya sa Gwannatin Najeriya ba Shigo-shigo ba Zurfi ne take yi wa ’yan kungiyar Boko Haram ba. Daga Zaidu Bala kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. 07037697009.

Shawara ga Gwamna Shema
Na rubuta wannan sako ne ga Gwamnan Katsina Dokta Ibrahim Shehu Shema, dangane da wata muhimmiyar dama da take samuwa ta wuce a Katsina, wannan dama ce wacce za ta amfani al’umma dangane da irin yadda burin ka shi ne sama wa al’umma abin yi kamar kwatan kwacin yadda ka kirkiri [craft billage] wato wurin koyar da matasa sana’o’in hannu to ga itatuwan mangoro da tsiron kan kana da suke samuwa a duk lokacin su, don hakan ni ke fatan za a dubi wannan shawara tawa a duba yuwuwar gina masana antar sarrafa ’ya’yan mangoro. Allah yasa wan nan tunatarwa ta zamo mai amfani ga al umma, Daga mukhtar ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519-08080140820.

Ga Karota
A kawo mana dauki. Edita don Allah ka isar min da kukana ga mai girma Gwamnan Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, a kasuwar Darki a Jihar Kano. Domin su gyara mana cunkoson motoci a kan titin Maiduguri. Abin ya fi karfin ’yan sanda sai dai ’yan KAROTA. Ina fatan za a duba wannan korafi nawa. Daga Ali Fancy Garko a Kano. 0815658950.

Fata ga Najeriya
Akwai wata hanya mafificya kuwa? Wane likita ne zai mana maganin wadannan tagwayen musifu na cin hanci da rashawa? Lokacin da sojoji suka kar be mulkin kasa nan sun yi alkawarin murkushe cin hanci da rashawa, amma yaya batun yake ne a yanzu?. Daga Jagoran Wayar da kan matasa na arewacin Najeriya, Auwalu Makarkata dambatta 08102661967.

Ga Manyan Arewa
Assalamu alaikum. Mutane uku sai sun hada kai, wato sarakuna da malamai da mawadata. Ku hada kai don kyautata rayuwar al’umma. Ku ji tsoron Mahaliccinku. Ga zaben 2015 yana karatowa. Daga Muhammad Siraju As-Salafy Agege, Legas 07065022222.

Ga Aminan Aminiya
Edita me yasa aka nuna mana bambancin bayan kuma mun san Aminiya ta kowace, ko kuma, ba mu iya Hausa bana Daga Abdullahi Muhammad Zariya K/Kona 07035329833.

Ga Janar Buhari da Sardaunan Kano
Zuwa ga Edita don Allah a mika min gaisuwa ga Janar Buhari da Sardaunan Kano, Shekarau Allah Ya kara mana lafiya. Amin. Daga Ruky Bala Fagge 08077788951

Ga Aminan Aminiya
Edita ga mika min godiya ga Aminan aminiya. Daga Hajara Azare, Jihar Bauchi 07034822558.

Ta’aziyya ga Media Trust
Inna lillahi wa inna ilahir raji’un. Ina mika ta’aziyya ga iyalan Editan Media Trust, Mallam Suleiman Muhammad Allah Ya gafarta masa amin. Daga Muhammad Sir TK Keffi Jihar Nassarawa 08036182362.

Ta’aziyyar mutanen Tsafe
Aminiya ki ba ni dama in mika ta’aziyyata ga mutanen da suka rasa rayukansu a Tsafe. Allah Ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Mu kuma Allah Ya kyauta karshenmu. Daga Nuraddeen Isma’il Gusau. 08105096009.

Ga Sardaunan Kano
Edita ka isar mini da sakon taya murna ga Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, bisa cikar Maimartaba Sarkin Kano shekaru 50 a kan karagar mulki. Allah Ya jikan Hajiya Mai Babban daki da Sarki Alhaji. Daga danladi Hafizu Sabi’u PRP GAMA C, Kano 08028912860.

Ina ayyukan alheri a Kano
Salaam, Edita ni dai ban ga kyawun wuri a ido ba, domin kuwa ga hasken fitilun da aka kashe kudi mai tsoka akan tiotunan da babu kowa a kansa da dare, amma an gaza wajen samun isasshiyar wutar lantarkin da za a sanya a dakin ajiyar gawa na asibiti; sai gawarwakin al’umma ke rubewa. Wadannan su ne ayyukan alherin da ake malalowa a Kano? Daga 08180814317.

Ga shugaban direbobi na Kaduna
Muna taya sabon Shugaban kungiyar direbobi ta NURTW na Kaduna, Alhaji Alassan 313 murna bisa samun nasarar zama shugaban kungiyar na jiha. Allah Ya taya riki, Ya ba da ikon yin aiki da gaskiya, tare da adalci ga jama’a. Daga Umar Mai Jalingo B.G. 07068307942.

Ga Gwamnan Zamfara
Yabon gwani ya zam dole. Aminiya ki ba ni dama in yabi jagoranmu, Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji AbdulAziz Yari, bisa gudunmuwar da yake bai wa yankunan karkara. Daga Malam Kabiru Hamdala GRA 08066272283.

Ga Janar Buhari
Janar Muhammadu Buhari muna kara jinjina maka akan hakurinka, don haka ka kara hakuri. Allah Yana tare da masu hakuri. Daga Sani abdu Beta 07068223015.