Kyaftin Shehu Iyali, tsohon mai tuƙa jirgin shugaban ƙasan Najeriya ya rasu.
Marigayin ya kasance mataimaki na musamman kan sufurin jiragen sama a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Kyaftin Shehu Iyal ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya yi fama da jinya.
Kafin rasuwarsa shi ne shugaban kamfani jiragen sama mai suna Afri Air.
Marigayin yakasance jigo a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya kuma ya tuka shugabannin ƙasa.
- Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa
- NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027?
A shekarar 1977 Kyafin Shehu Iyal ya kammala karatun digiri ɗinsa a Jami’ar Ahmadu Bello kafin daga bisani ya shiga Kwalejin Koyon Tuƙin Jiragen Sama (NCAT) da ke Zariya.
Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamai da dama a fannin sufurin jiragen sama har da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa a matsayin mai kula da sashin zirga-zirgar jirage na hukumar.
Bayanai daga iyalan marigayin na nuni da cewa za ayi jana’izar Kyaftin Shehu Iyal a yau Juma’a da yamma a unguwar Ƙwarbai cikin birnin Zariya.