Musulunci addini ne kammalalle kuma kubutacce daga kuskure ko tawaya. Binciken masu bincike ke sadar da su ya zuwa ga ilmin yakini akan ingancin sakonnin da ke cikin Alkur’ani mai girma. Hankali na da gagarumin gudummawar da yake bayarwa wajen samun ilimin yakini a cikin ko wanne fage na ilmi, don haka ne ma Allah (swt) ya muhimmantar da hankali wajen fahimtar Alkur’ani mai girma. Ke nan hankali ne ma’aunin tantance gaskiya da karya, rawar da nassi ke takawa kawai shi ne saukaka wa hankali riskar hakikanin da zai dade bai riska ba, ko kuma zai kuskure riskarsa. Makomar ko wanne nassi kuwa shi ne Manzo (s), da ma’anar cewa ko wanne nassi na tabbatar da manzancin manzo(s) ne, kamar yadda manzo(s) ne ke tabbatar da ingancin kasancewar nassi daga Allah (swt) yake. Da haka ne za mu fahimci cewa babu inda hankali ya saba wa sakon Musulunci bare Shari’ar Musulunci, kamar yadda babu inda sakon musulunci ko Sharia’ar Musulunci ya saba wa hankali.
Albarkacin hankali ne ya sanya musulunci ne kadai fikirar da ke iya samar da amsa ga duk wata matsala ko shubuhar da ke kaikawo a cikin rayuwar ‘yan Adam cikin sauki ba tare da wani bangaren rayuwar wani dan Adam ya cutu ba. Musulunci na fuskantar barazana ta fuskoki guda biyu, duk da kariyar da ya yi wa ilmi ta hanyar sanya hankali a matsayin katanga ga jahilci. Musulunci na fuskantar barazana ne daga makiyansa na cikin gida da kuma makiyansa na waje. Duk inda jahili yake makiyi ne ga Musulunci ko da kuwa musulmi ne. Jahilan Musulmi ne makiyan musulunci a cikin gida. Duk wanda ba musulmi ba kuma yake sukan musulunci lallai makiyi ne na waje. Nazari ya nuna cewa makiyi na waje bashi da karfin gwiwar sukan musulunci har sai makiyin cikin gida ya soki musulunci. Jahilan musulmi kanyi rubuce-rubuce na sukan musulunci cikin jahilci ba tare da sanin sunayi ba, ko da yake jahilcin nasu ya rufe masu ido har ta kai ga suna ganin bajinta suka yi wajen kare Musulunci, ta hanyar rubutun nasu.
Wani al’amari da yake teburin ‘yan majalisar dokoki na Najeriya shi ne; shekaru 18 ne mafi karanci wajen aurar da ‘ya mace. Hakan kuwa na da nasaba ne da auren ‘yar shekara 13 da Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya yi. Nayi sha’awar yin rubutu da harshen hausa ne akan wannan al’amarin daga lokacin da nayi kicibis da rubutun da Nasir Abbas Babi ya yi a cikin jaridar Aminiya ta ranar juma’a, 16 ga Agusta, 2013 a shafi na 11, mai taken “shin ya kamata a zagi Yariman Bakura?” Lallai ya yi rubutu mai tsafta, inda ya bayyana ra’ayinsa ta hanyar bijiro da shubuhohin da amsarsu basa zama dalili ga auren ‘yar shekara 13 da Yariman Bakura ya yi, mai makon hakanma amsarsu na kalubalantar auren da Yariman Bakura ya yi ne. Abin da ya fi jan hankalina wajen yin wannan rubutun kuwa shi ne, inda Nasir Abbas Babi ke cewa “…Yarima ya yi wata sunna daga cikin sunnonin manzon rahama mai tsira da aminci,…” wannan zancen a kaikaice na karfafa marubutan da ke ta sukan Manzo(s) ne da sunan Yariman Bakura ya auri ‘yar shekara sha 13. Wannan na nuni ne da cewa Musulmi ne suka nuna masu hanyar da za su bi wajen bata shaksiyyar manzo(s).
A babin misali, a kafafen jaridun da ke Jihar Ribas, akwai marubuci Samuel P. Amadi da ya yi rubutu a jaridar The Tide ta ranar Laraba, 31 ga Yuni, 2013 da Franklyn Inwokwocha da yayi nashi rubutun a jaridar Plain Truth ta ranar Juma’a, 2 ga Agusta, 2013 da kuma rubutun Benjamin B. Pepple da ya yi a jaridar The Neighbourhood ta ranar Alhamis, 15 ga Agusta, 2013. Wadannan marubutan sunyi rubutunsu ne don kalubalantar wasu musulmi da suka yi rubutu a jaridar The Nation da kuma jaridar The Sun da nufin nuna ingancin auren da Yariman Bakura ya yi, har suka alakanta auren da wasu hadisai da ke nuna manzo(s) ya auri ummul mu’minin, A’isha tana ‘yar shekara shida. Marubutan sun yi amfani da kalmomin da ke muzanta manzo(s), kalmomine da ke fassara abin da musulmi suka jingina wa manzo(s) akan aurensa da Ummul Mu’minin, A’isha. Ka ga ke nan ‘in bera da sata, to lallai daddawa ma da wari.’
Lallai Manzo(s) ya auri ummul mu’minin, A’isha, amma ga duk mai sakakken ra’ayi da tunani, in ya yi tadabburi da tafakkuri a cikin hadisan da ke ishara ga shekarunta na lokacin auren zai cimma babu daya daga cikinsu da ya inganta ta fuska cikin isnadinsa da mataninsa. Rashin ingancin wadannan hadisan ya fi fitowa fili ne sosai in kayi la’akari da cewa tarihi na taka gagarumin rawa wajen tantance ingancin ko wanne irin labari. Duk hadisan da ke magana akan shekarun Ummul Mu’minin, A’isha 6 ne a lokacin auren, sannan ta tare tana ‘yar shekara 9 ba su inganta ba, a ka’idar ingancin hadisi a gun malaman hadisi. A babin misali, kusan daukacin hadisan da ke isharar shekarun A’isha a lokacin aurenta da Manzo(s) sun fito ne daga Hisham ibn Urwa a lokacin da yake zaune a Iraki, wani abin burgewa shi ne malaman Jirhu wal ta’dil sun tafi akan cewa hadisansa ingantattu ne banda wadanda aka ruwaito a Iraki. Hakan ya nuna duk hadisansa da aka ruwaito a Iraki suna da illa. Da wannan ne nake cewa masu yi wa Manzo(s) karyar ya auri ‘yar shekara shida (6) su tanada wa kansu masauki a lahira, don yi wa Manzo(s) karya ba abar wasa bace.
Abin lura na biyu da ke tabbatar da Rashin gaskiyar zancen cewa Manzo(s) ya auri Ummul Mu’minin A’isha tana ‘yar shekara shida (6) ba gaskiya ba ne shi ne; babu jayayya a tsakanin malaman tarihi cewa Asma’u ya ce ga A’isha, kuma ta girmi A’isha da shekaru 10 ne, sannan ta rasu a shekarata 73 bayan hijra ne tana ‘yar shekara 100. Yanzun a bayyane lamarin yake cewa Asma’u na da shekaru 27 kafin hijra, tunda kuwa ta girmi A’isha da shekaru 10 ke nan A’isha na da shekaru 17 ko 18 ne kafin hijra, sannan ta tare a gidan Manzo(s) tana ‘yar shekara 19 ko 20. Da wannan ne nake cewa masu yi wa Manzo(s) karyar ya auri ‘yar shekara 6 su tanada wa kansu masauki a lahira, don yi wa Manzo(s) karya ba abar wasa bace.
Wadannan su ne wasu daga cikin dalilai 43 da ke tabbatar da rashin ingancin ruwayoyin da suka shahara akan shekarun A’isha yayin aurenta da Manzo(s). Alamomi na nuni da cewa ba al’adar Larabawa ba ce aurar da ‘ya’yansu mata a kasa da shekaru 9, Manzo(s) kuma bai auri A’isha tana ‘yar shekaru 9 ba. Nasihata ga masu kare kuskuren da Yariman Bakura ya yi na auren ‘yar shekara 13 da sunan addinin Musulunci shi ne ku rika fadada bincike akan lamurran addinin Musulunci kafin ku yi gigin rubutu akansa. Rashin yin tadabburi da tafakkuri a cikin lamarin ya haifar maku da kare wanda ya cancanci zargin dukkan mutane, aljanu da mala’iku. Ku kiyayi yi wa Manzo(s) karya da sunan kare Yariman Bakura, don sakamakon hakan tanada wa kanku matsuguni ne a wuta.
Da fatan wannan ya wadatar mu iya fahimtar kuskuren jingina wa Manzo(s) auren ‘yar shekara 9, kuma hakan ya samar da fahimtar daidai din majalisar dattijai wajen kayyade shekarun mace a lokacin aure ya soma daga shekaru 18.
Yushau Muhammad Lawal (07067379445)
Dalibin Mechanical Engineering a
Pan African Institute of Management and Technology, Fatakwal, Jihar Ribas.