✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani ga Mai dankoko

Salam Martani ga Ahmad Mai dankoko, ka yi kuskure, kuma ka yi son zuciya. dabi’ar izala da furucinta ke kafirta kanta da  kuma jama’a. Ga…

Salam Martani ga Ahmad Mai dankoko, ka yi kuskure, kuma ka yi son zuciya. dabi’ar izala da furucinta ke kafirta kanta da  kuma jama’a. Ga hujja kamar haka, kun ce duk wanda ba ya izala ba Musulmi ba ne. Shin Annabi ko sahabbai sun yi izala? Gumi ya ce siyasa ta fi salla; kun ce Annabi (SAW) mutum ne kamar kowa. Ba za ku yarda ku ce Sani Y. Jingir mutum ne kamar Goodluck ba, ba ku cewa Sayyidina Rasulallahi, amma kuna cewa Shugaban majalisar Malamai. Kun ce ’yan darika mushirikai ne, amma kuna cin gadon dukiyarsu. Ina ruwan Musulmi da gadon Mushiriki? Kun raba masalaltai, amma ban da makabarta. Idan za a shiga izala ba a wanka Daga Sa’idu dan Kanam Gora Jihar Nassarawa 08150526798

Ina aka sa gaba a Jihar Kebbi
Assalam Edita, ina son ka ba ni dama in yi magana kan siyasar Jihar Kebbi, domin mu ba mu gani ba, ba mu san inda aka sa gaba ba. Don haka gwamna ya yi mana bayani. Daga dangaladima Naira Kangiwa 07038339623.

Ga matasan Makarfi
Assalamu alaikum, a gaskiya matasan karamar Hukumar Makarfin Jihar Kaduna na ba mu kunya. Bai kamata a ce yadda garin Makarfi ya samu ci gaba a halin yanzu, a ce matasa bas u da abin yi sakamakon zaman banza da kuma shaye-shaye. Da ma Hausawa sun ce idan kaga tsohon banza asalinsa yaron kirki ne. Ina bai wa matasa shawara a dage da neman ilimi, a kuma kama sana’a. Daga Yakubu Mai Kemis Layin Rimi Makarfi 08034802315.

Ta’aziyyar Madakin Lafia
Muna mika ta’aziyyarmu ga ’yan uwanmu mutanen Lafiyar Barerbari kan babban rashin da suka yi na Madakin Lafia, Alhaji Malam Auwal Yusuf Musa. Allah Ya jikansa, Ya tabbatar da rahama a gareshi. Daga Mutanen Gala, Jihar Barno. 08104395016

Ga Hajiya Talle
Shawara ga Hajiya Talle Muhammad Hadeja. Daga cikin abubuwan da za su sa ta zama gawurtacciyar ’yar siyasa: ta yi aure don Allah, ta yi adalci, ta kara hakuri; ta zama mai tausayi. Ta rika tallafa w amatan aure. Daga 08089190590

Allah Ya ba mu shugabanni nagari
Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa. To ’yan Najeriya; mahakurci, mawadaci. Allah Ya ba mu shugabanni na kwarai. Daga Brazilian Sambo Abuja 08036865813.

Sako ga Jam’iyyar APC
Assalamu alaikum. Aminiya zuwa ga ’yan APC, ya kamata kusan ba ko’ina za ku shiga ku yi karantsaye ba. Gombe da haka ta faru, da ku jama’a sun fara nuna muku cewa ba sa son rikicin da kuke hadama a jihohi. Kuma idan kun zo Josh aka za mu yi muku. Domin abubuwan da kuke yi ba don talaka ba ne, domin bukatun ku ne kawai. Daga Alhaji Sale Zazzaga Jos Bukur. 08036345317

Jinjina ga Gwamna Sule Lamido
Edita ka ba ni dama in mika sakon jinjinata ga dan Masanin siyasa kuma jagoran siaysar  Najeriya Jam’iyyar PDP, Gwamnan Jihar Jigawa, Dokta Sule Lamido. Allah Ya yi ma jagora. Daga Bello Dandinb Mahe Suleja 08034275846.

Martanin murnar Kirsimeti
Salam na samu sako da kira akalla 50 daga sassa na Arewacin Najeriya, kamar Kaduna da Zamfara da Kano da Gombe, wai kan mu tura sako murna kirsimeti ga Kiristoci, wai wani ma har cewa ya yi yana da inkari kan Musuluncina. Addini zaman lafiya ne, ku tafi ku duba littatafai. Muna rokon Allah Ya kara mana imani. Daga Mu’azu Safiyanu danja 08054639924.

Gaisuwa ga Tambuwal
Gaisuwa Ga Aminiya don Allah ku mika min gaisuwa ga jikan Mujaddadi Usmanu, kuma shugaban kasar Gobe. Tambuwal Sarkin Yakin Daular Usmaniya. Don Allah ka dawo gida ka yi mana gwamna 2015. Daga Murtala  Amwa Sakkwato 07050868840.

Ga Talban Minna
Salam Edita don Allah ina so ka ba ni dama kadan zan yi magana a kan Gwamna Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, Talban Minna, ya fuba da ilimi da hankali da mulkin Allah Ya ba shi; Ya tujna akwai mutuwa, akwai hisa. Gwamna hana kabu-kabu da ka yi a Neja bai yi ba. Daga Iliyas Idris Fahad Suleja 08153330627.

Murnar sabuwar shekara
Aminiya ba ni dama in yi wa daukacin al’umamr kasar nan murnar shiga sabuwar shekarar 2014. Da fatan Allah Ya b amu zaman lafiya a kasar nan baki daya. Daga Ibrahim KSD 08031944943.

Gaisuwa ga Sadiya gyale
Assalamu alaikum, Aminiya ina so a mika min sakon gaisuwata ga Sadiya gyale, babbar jaruma a cikin masoya fina-finan Hausa. Daga Nasiru Muhammad (wafa) Sakkwato 08031914141.
Kira ga ’Yan Arewa

Kirana ga ’Yan Arewa, mu yi hankali da Obasanjo da yaransa. Haka suka yi wa ‘’Yar’aduwa har suka kais hi kar. Daga 08039107554.

Ga Muhammadu Buhari
Aminiya ku aika min sakona zuwa ga Janar Buhari.; Daga Hussaini Kambaza 07036306540

Rahama ga ’yan Najeriya
Edita barka da fama. A askiya mu ’yan Najeriya duk wanda aka haife a wannan zamani, kuma a cikin irin wadannan shugabanni, to in ya mutu muna yi masa tsammanin samun rahama. Daga Sani abdu Beta 08178112034.

Aminiya kun ji kunya
Aminiya kun ji kunya, watan mauludin Annabi Muhammad (SAW) ya kama kuka kasa rubuta komai akai! Wannan ya nuna ba ku da kishin Mamnzon Allah (SAW) Daga Alhajiji Fagge  08028185611

Kuka ga Aminiya
Don Allah Aminiya na turo sako ba ku sa ba, kuma duk Juma’a sai na sayi Aminiya, ba a barina baya.. Daga Muhammad Nuhu Bwari, Abuja 08050760340.

Gwamna Yero ka ziyarci Kano
Gaisuwa ga ma’aikatan Aminiya. Shawara ga Gwamna Yero na Jihar Kaduna, ya kamata ya ziyarci Jihar Kano don yin koyi, ko har yanzu ba a rantsar da kai ba ne? Daga Musanam Ustaz 08156572079.

Ta’aziyya ga mutanen Kwankwaso
Salam, Editan Aminiya ka isar min da sakon ta’aziyyata ga al’ummar kauyen Kwankwaso da Mai martaba Hakimin Madobi, Alhaji Musa Sale da Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, a kan harin da ’yan bindiga suka kai w akauyen. Allah Ya jikansu, ya yi musu rahama amin. Har way au ina jajanta wa wadanda suka jikkata. Daga Hussaini M. Zamfara Fct, Abuja 08111297503.

Mu yi kuka da manyanmu
Salam munafinci dodo yakan ci mai shi. Mutanen arewa duk halin da Arewa ta shiga a yau kada mu yi kuka da kowa, mu yi kuka da manyanmu; su suka sayar da ’yancin Arewa, saboda rashin kishi da son abin duniya. Daga Mai kishin talaka Jamil Fagge, Angon Zahra’u Mazaunin Legas 08032372896.