✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani ga Kabiru Gombe

Salam. Don Allah Edita ina so ka ba ni dama in yi wa Kabiru Gwambe martani a kan sakonsa da na gani a wannan jaridar…

Salam. Don Allah Edita ina so ka ba ni dama in yi wa Kabiru Gwambe martani a kan sakonsa da na gani a wannan jaridar taku. Zancenka bai ban mamaki ba, tunda Ma’aiki (SAW) har ya yi wafati akwai amsu yi mas hassada, ka ga kuwa dole ne masoyansa na hakika su samu masu yi musu hassada. Don na lura ba komai yake damunka da mabiyanka ba, face hassada da kyakkyawan karshen da Fadar Bege ya samu. To ka sani ,shi wanda kake wa isgili da ‘Wali mai ganga,’ tashi ta kare, kuma tun a duniya ya samu shaida mai kyau. Kuma in dai don muna yabon Ma’aiki (SAW) shi ne muka zama abin a zaga, to ka sani sara da sassaka ba sa hana gamji tofo. A karshe in mai baka shawara da ka ji da abin da ke gabanka, wato mutuwa, don shi fada, tuni ya dade da isa fadar masoyinsa, wato Ma’aiki (SAW). Don Allah Edita a sa min sakon nan. Daga Fatima I. Usman Kano 08133296624.

Sakonnin waya

Ta’aziyya ga mutanen Barno
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ki mika min sakwon ta’aziyya ga al’ummar garin Barno. Allah ya tona asirin wadannan mutane. Allah Ya kare sauran musulmi baki daya. Amin. Daga Sa’adatu Zayyanu bodinga 08132785679.

A daina tsine wa shugabanni
Salam Aminiya Edita ka ba ni dama in sanar kan a daina tsine wa shugabanni. Kamata ya ui idan mun yi ibada mu riga rokon Ubangiji Allah ya ganar da mu da su a kan hanya madaidaiciya. Daga Gimbiyar Aminiya 08066096549.

Kwanakinmu na karewa
Salam. Ya ’yan uwa Musulmi mu lura yadda rayuwarmu ke karewa da gari ya waye sai ka ga dare ya yi. Shekara ta zama tamkar wata, wata kamar mako, mako kamar yini, yini kamar sa’a, sa’a kamar mintuna. Mu yawaita bautar Allah da biyayya ga iyaye; da salla kan lokaci. Daga Ummul Khaeery Kaduna. 08147933176.

Ta’aziyyar Albani
Salam Aminiya fatan alheri gareku. Ina son a mika min sakon ta’aziyyata ga iyalan MArigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani. Allah Ya jikansa, Ya yi masa rahama. Amin. Daga Husnah Dabay 07068514071.

Ta’aziyya ga limamin Saudiyya
Salam Aminiya ku mik amin ta’aziyyata ga Babban Limamin kasar Saudiyya, wato Sheikh Al-sudais. Allah ya jikan mahaifinsa da al’umamr Musulmi. Amin. Daga Maman Fati Gombe 07069453687.

Ta’aziyyar Albani
Salam. Ina mika sakon ta’aziyyar Malam Albani a dukkan ’yan uwa ahlussunnah da iyalansa. Allah Ya yi musu rahama, ya tona asirin makasansu; Ya kuma tsare Malaman sunnah a duk inda suke. Daga Amina Abubakar U/Yari KT 08069185007.

Ta’aziyyar Albani
Edita da sauran ma’aikata a mika min ta’aziyyata ga dukkan musulmi ’yan uwa da da iyali da dalibai bisa rasuwar Sheikh Albani, Allah Ya jikanshi da rahama, Ya ba mu hakurin rashin babban malami mai dimbin ilimi. Daga Hauwa’u Sada Yusuf 08050236145.

Allah ya yi wa zawarawa zabi
Salamun alaikum. Zuwa ga Aminiya, mu dai zawarawa muna kai kukanmu ga Allah Ya zaba mana mazaje nagari. Don duk bazawara tagari ba za ta so zama haka ba. Nagode. Daga Zainab S. Isah Kano 08131832802.

Ka yi daidai Shekarau
Salam Edita ka isar mini da sakona  ga Sardaunan Kano, Dokta Malam Ibrahim Shekarau, ka yi daidai da ka bar APC ka koma PDP. Dama Hausawa sun ce ‘siyasa rigar ’yanci. Daga Baban Misis Gandun Albasa, Kano 08067683754.

Ga majalisar Malamai
Salam Edita, a mika gaisuwata ga shugaban majalisar malamai na kasa, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukum da Alhaji danladi mai kaset Jos. Allah Ya kare mana ku. A ci gaba da yada addinin Musulunci. Daga Khadija Tawakaltu sagari Kona 08149695228.

Ga Gwamnan Katsina
Edita don Allah ina so ka mika min sakon taya murna ga Gwamna Ibrahim Shehu Shema, sakamakon nadin sarautar da aka yi masa na Sarkin Fulani. Allah Ya taya shi riko. Amin. Daga Aisha Yusuf dalhatu Gwarzo 08130205348.

A karrama Sadi Sidi Sharifai
Salam gaisuwa da jinjina a gareku aminaina, gaskiya ya kamata a bai wa Sadi Sidi Sharifai lambar yabo Award a kan wakarsa ta nass ciwon so. Daga Aisha A. Adam Zariya 08033272211.

Ko ana biyan kudin sako?
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ina son ku sanar da ni idan akwai wasu kudi da ake biya kafin ku buga sakon mutum, domin na sha aiko da sako, amma ba ku taba bugawa ba. Daga Murtala I. Mohammad Abuja 08098964491.

Addu’a ga mutanen Barno
Al’ummar Barno na cikin wani hali mu taimaka musu da addu’a. Shi ne kawai abin yi. Daga Idris Suleja 08059265482.

A yi adalci Aminiya
Aminiya ku rika adalci mana ko kuma ’yan APC ne? Rabon da ku buga sakona an fi wata shida. Daga Isyaku Captain Kofa Masoyin Sardaunan Kano, M. Ibrahim shekarau 08067226769.

Addu’a ga Aminiya
Assalamu alaikum, da fatan Allah (SWT) ya saka muku da  alkhairi, saboda tunatarwar da kuke yi wa al’ummar Musulmi, da fatan Allah (SWT) ya kara muku basira da kariya. Amin. Daga dan uwanku Auwaliu Sani Potiskum. 08104612945.

korafi ga Aminiya
Haba Aminiya inji dai ba laifi na yi muku ba? Saboda na rubuto sako da yawa, ama ba ku buga ba. Daga Abdul C.A.C. H/kuarters, Abuja 08099906986.

Ga masu turo sakonni
Ina kira ga masu turo sakonni, don Allah mutum ya san irin kalaman da zai aiko, masu ma’ana da inganta tunanin al’umma. Kuma Edita duk wanda bai sanya adireshi da lambar wayarsa ba, kada a buga sakonsa. Allah Ya rufa mana asiri duniya da lahira. amin. 08026392800.

Sakona tun 2013
Salam Editan Aminiya mai farin jini tun 2013 rabonku da sakona. Ba rashin buga sakon ya sa na daina ba. A dai mika min sakona ga daliban makarantar UZK koki Kano Candy 2011. Daga Teemah Fagge 07034888424.

Malam Shekarau ka yi hakuri
Editan Aminiya ka ba ni fili a jaridarka in fada wa mutanen Kano cewa shigar Malam Shekarau PDP alheri ne a gare ku, domin masifar APC sai ta dame mu, ko kuma ka ga ‘yan APC sun koma gun Shekarau kafin zaben 2015. Mal. Ka yi hakuri za su dawo gunka ion sha Allahu. Daga Hon. Auwalu  Datti Gumel 08058412652.

Ga Talakan Najeriya
Mu yi wa kanmu fatan alkhairi da shugabanni. La’ance-la’ance ba zai kai mu ko’ina ba, sai nadama. Daga Aliyu Abubakar Harbo 08056444726.