Wani maroki mai suna Alhaji Sabo Mai Kukuma ya rabauta da kyautar mata bayan makudan kuɗin da aka bashi yayin bikin karamar salla a Fadar Sarkin Hausawan Mararaban Gurku, Alhaji Adamu Usman Mani.
Dan Malikin Sarkin Hausawa, Muhammad Mubarak Jalo ne ya bayyana bai wa Alhaji Sabo Mai Kukuma kyautar Mata.
Ya sanar da hakan ne jim kaɗan bayan Alhaji Sabon ya kammala wasa a filin Kasuwar Ƙasa da Ƙasa ta Muhammadu Buhari da ke Maraban Gurku a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Mai martaba Sarkin Hausawan Mararaban Gurku, Alhaji Adamu Usman Mani ne ya shirya gagarumin bikin domin taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Dan Malikin Sarkin Hausawan ya bai wa Alhaji Sabo Mai Kukuma zabin mata ko sadaki, inda ya ɗan yi jim kaɗan, sai Alhaj Sabo ya ce a ba shi mata.
Nan take Sarkin Hausawa ya rada wa Dan Malikin nasa cewa, an bai wa Mai Kukuma mata.
Alhaji Sabo wanda ya bayyana mana cewa an yi masa kyautar kujerar aikin Hajji, an ba shi gida an ba shi mota, amma wannan kyautar ta fi kowacce girgiza shi.
Wasu daga cikin rawunnan Sarkin Hausawa sun zanta da wakilin mu kan wannan biki.
Dan Malikin Sarkin Hausawan Mararaban Gurku, Muhammad Mubarak Jalo ya bayyana irin wannan biki a matsayin wata alama da ke nuna yadda kan al’ummar Hausawa ke haduwa a garin.
“Hakika irin wannan biki yana nuna cewa uwarmu daya ubanmu daya, muna fata Allah Ya maimaita mana”.
Alhaji Abdullahi Ibrahim Gwandu, Makaman Sarkin Hausawan Maraba ya bayyana bikin a matsayin kyakkyawar al’ada.
“Wannan itac e al’adar mu. Rashin irin wadannan wasannin ke sa ‘ya’yanmu sha’awar al’adu da dabi’un wasu da ba su kai namu kyau ba”.
Ya bayyana bai wa irin wannan al’adu goyon baya a matsayin hanyar kawo gyara mai ɗorewa a tsakanin al’umma.
Yakubu Bello Malam Baba Sarkin Malaman Mararaban Gurku, ya bayyana taron a matsayin wani makami na tarbiyyar yara..
Ya ce, “Ana yi wa wannan gari namu kallon bariki, amma ba bariki ba ne, domin kuwa yanzu mun assasa wani abu da zai ɗebe wa yaranmu kewa ta hanyar da ta dace”.
“Ina kira ga daukacin al’ummar Hausawan wannan gari su zo mu haɗa kai domin ci-gaban mu baki daya”