✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marigayi Sardauna Ahmadu Bello: Ba rabo da gwani ba…

Yau kimanin shekaru hamsin da suka gabata Allah Ya amshi ran jangwarzo.

A ranar 15 ga Janairu na shekarar 1966 aka yi wa Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Arewa kisan gilla, sai dai har zuwa yau, kwarjininsa da ayyukan kirkin da ya shimfida a kasar nan suna ci gaba da haskakawa.

Dalili ke nan da a yau, marubuci MALAM IS’HAKA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858), mai adireshin I-mel: [email protected] ya rubuta wannan tsokaci a matsayin tunawa da shi.

Ga abin da yake cewa:

Allah mai yadda Ya so! Mutanen duniya kowa yana da sha’awar shiga aljanna amma babu mai sha’awar mutuwa.

Idan ana ba da labarin wani mutum mai halaye na gaskiya, adalci da rikon amana, sai ka rika sha’awarsa amma mai ya sa kai ba ka iya daukar matakin da za ka kai fagen da wancan mutum ya kai, ko ma ka yi fiye da adalcinsa, gaskiyar da rikon amanarsa ko da a mulkin iyalinka?

Duk mutumin da Allah Ya sa yana raye a yau a Arewacin kasar nan, kuma shekarunsa ba su kasa ga arba’in da haihuwa ba, ya samu akalla takaitaccen labari, tarihi na wane ne Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jihar Arewa.

Ko dai labarin ya samu ne a kafofin yada labarai ko jaridu ko kasidu ko littattafai ko wakokin Hausa ko radiyo ko talabijin ko a muhimman gine-gine ko kuma kunne-ya-girmi-kaka.

Marigayi Sa Ahmadu Bello, Firimiyan Jihar Arewa na wancan lokaci, jihar da a yau aka yanka ta, aka kirkiro jihohi goma sha tara da ke kunshe da kananan hukumomi 407.

Matsayin da Sa Ahmadu Bello ya rike ya kai a kwatanta shi da na Firaminista ko Shugaban Kasa ga mutanensa na Arewa.

Yau kimanin shekaru hamsin da suka gabata Allah Ya amshi ran jangwarzo, jarumi, adali, mai gaskiya Sa Ahmadu Bello, da ’yan ta’adda suka harbe da bindiga a ranar 15 ga watan Janairu, 1966 a gidansa.

Mutumin da a kullum kewarsa na zukatan al’ummarsa na Arewa, domin adalcinsa da nasarorin da ya samu a lokacin wa’adin mulkinsa na Firimiyan Arewa.

Ya kamata mu lissafa kadan daga cikin ayyukan raya kasa da adalci da kyakkyawan jagoranci na Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello domin mai karatu ya sani ko da ba zai yarda ba.

Wasu daga nasarorin da Firimiyan ya samu sun hada da: Gudummuwarsa kan harkokin ilimi, inda ya ba da umurnin gina makarantun firamare da sakandare har da na gaba da sakandare da jami’a.

Daga cikin makarantun da ya kaddamar da bikin bude su har da Makarantar Horon Malamai ta Wudil, a ranar 27 Nuwamba 1965.

Ya bude Kwalejin Horon ’Yan sanda ta Kaduna a ranar 30 Nuwamba, 1963.

Ya bude Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Polytechnic), da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru, Zariya ranar 11 Oktoba 1962.

A fannin ruwan sha da noma ga jama’a, Firimiya ya gina madatsun ruwa domin noman rani da kiwo da ma’aikatun ruwa da rijiyoyi a lardunan Arewa.

Ya kaddamar da bude Ma’aikatar Ruwa ta Daura a ranar 23 ga Nuwamba, 1960. Ya bude Ma’aikatar Ruwa ta MandoKaduna a ranar 25 ga Maris 1960.

A fannin lafiya, Firimiyan ya gina asibitoci a larduna da asibitin kashi guda daya tilo a Dala da ke birnin Kano a ranar 21 Disamba1959.

Asibitin da ya dauki nauyin kula da majinyata kashi daga jihohin Arewa goma sha tara, a tsawon shekaru arba’in da biyar bayan kafa shi.

Bayan wannan shekaru an samu wasu gwamnoni uku ko hudu da suka gina asibitocin kashi a jihohinsu.

A fannin tattalin arzikin kasa, Firimiyan Arewa ya gina bankuna, ya bude Bankin Baclyas da yanzu ake kira Bankin Al’umma (Union Bank) na farko a Arewa a ranar 15 Satumba 1956.

Haka ma shi ne ya bude bankin Arewa (Bank of the North) da aka mai da shi Unibersal Bank. Ya bude Hukumar Wutar Lantarki ta Arewa (ECN) a garin Bida a ranar 1 ga Janairu 1961.

Ya kuma bude otel din Hamdala da ke garin Kaduna a ranar 27 ga Fabrairu 1960.

Sauran nasarorin da Firimiyan Arewa ya samu sun hada har da bude kamfanin buga jarida na Kaduna (NNN) da kamfanin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke birnin Zariya.

Haka kuma da kamfanin sumunti na birnin Sakkwato da Masakar Atamfa ta Arewa a Kaduna da ta Gusau da Gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna (Farin Gida) da filin wasa na Kaduna da sauransu.

Bisa ga kadan daga nasarorinda aka lissafa a baya, Firimiyan ya rike sakatarensa wanda ba addininsu daya ba, ba kabilarsu ddya ba, har tsawon karshen rayuwarsa.

A nan muna ta lalube mu samo daya daga hadimai ko abokai ko aminai ko ministoci ko abokan aikin Firimiya da ya dauki darasi daga dabi’u ko halayensa, ya aiwatar ga jama’arsa a matsayin da ya taba rikewa ko yake rike da shi a yau.

Mutumin da ba ya nuna kabilanci, mai gaskiya, mai rikon amana kamar na Firimiyan Arewa duk da cewa Firimiyan Arewa yana da ministoci guda goma sha bakwai da kananan ministoci bakwai a karkashin Jihar Arewa.

Kuma a lokacin Hukumar Kidaya ta Kasa a 1963 ta tabbatar da mutanen Najeriya su 55,620,268 ne, daga cikinsu Jihar Arewa na kunshe da mutum 29,758,875.

Yayin da Jihar Gabas na da mutane 12,394,462, sai Jihar Yamma da ke da mutane 10,256,846.

Sai kuma Yamma ta Tsakiya mai mutane 2,558,879. Legas na da mutane 665,246.

Bayan rasuwar Firimiyan Arewa, yau kimanin shekaru hamsin, muna cigiyar wanda ya rike mukamin jiha daya daga cikin jihohi goma sha tara, ko wanda ya rike mukamin Shugaban Karamar Hukuma daga kananan hukumomi 407 da Firimiya ya shugabanta a lokacinsa, da jama’arsa za su ba da shaidar ya yi adalci, ya dogara ga albashinsa, ya yi gaskiya, ya yi ayyukan raya kasa ga jama’arsa irin na Firimiya.

Duk da matsayin da Firimiyan Arewa ya rike na shugaban Jihar Arewa, ya rasu ba tare da ya bar abin da ya mallaka na kansa, ko ya sata ko ya kwace ko handama ko babakere na daga dukiya ko kudi ko motoci ko gidaje ko kamfanoni a kasarsa ko kasar waje.

A karshe dai gidansa biyu. Wannan ya yi daidai da jawabinsa, inda ya ce: “Na sadukar da kaina in yi aiki ba tare da gajiyawa ba, domin ci gaba da farin cikin sabuwar Arewa.

Na yi rantsuwa da sunan Allah idan har na rasu ba zan bar komi ba amma sai dai gwagwarmaya domin ’yanci, mutunci, da martabar kasar nan.”