Kungiyar cigaban garin Lawanti a jihar Gombe ta, Lawanti Community Debelopment Association ta bai wa marayu kimanin 513 kayan sallah.
Shugaban kungiyar Alhaji Abu Ubaida, a jawabinsa wajen raba kayan yayi kira ga al’umma da su dinga taimaka wa Marayu da ‘ya’yan marasa galihu dan rage musu radadin rayuwa a irin wannan lokaci na sallah.
Alhaji Abu Ubaida, ya jawo hankalin al’umma da cewa ka da a irin wannan lokaci mutane su yiwa ‘ya’yansu kayan sallah su manta da koda Maraya daya ne.
Yace duk shekara kungiyarsu tana bada irin wannan tallafi na kayan sallah da sutura da gidan sauro wa marayu amma yanzu saboda yanayi ya canja kayan sallah kawai suka iya bayarwa ba tare da sauran kayayyakin ba
A dan haka ya kirayi masu hannu da shuni da shugabani da su shigo su hada hannu da kungiyar cigaban garin Lawanti dan shiga aikin lada.
Shi kuwa Malami a jami’ar jihar Gombe, Malam Yusuf Ibrahim Talban Tabra, ya ce kungiyar cigaban garin Lawanti tana aiki wajen taimaka wa marayu wanda aikin alkhairi ne domin Annabi S.A.W ya ce duk wanda yake taimakon marayu za su ta shi tare a ranar gobe.
Talban Tabra, ya yabawa kungiyar cigaban garin na Lawanti saboda aikin sa kai da suke yi wanda aikin ne na neman lada.
Malam Yusuf Ibrahim, ya ce dan Yaro ya zama maraya ba shi kenan rayuwar sa ta kare ba, domin anyi shugabanin kasashe da dama da suka kasance marayu a duniyar nan.
Sannan sai yace taimaka wa marayu bai tsaya a iya sutura kawai ba, ya hada harda kulawa da lafiyarsu da kuma iliminsu.
Suleiman Abubakar dan shekara 13 da kuma Kaltume Habu ‘yar shekara 13 ita ma, marayu ne da suka ce basu da mai yi musu kayan sallah; da basu samu a wajen kungiyar ba, da ba yadda suka iya sai kallo.
Ita ma gidauniyar Zakka da Wakafi ta jihar Gombe ta raba kayan sallan da na kayan abinci ga kimanin yara marayu sittin maza da mata da manyan mata marasa galihu.
Da yake jawabi kafin mika kayan tallafin Shugaban gidauniyar na jihar Gombe Ustaz Abdullahi Abubakar Lamido, cewa ya yi wannan kayayyakin da suka bai wa Marayun, sun same su ne daga gudumawar masu hannu da shuni suka bayar.
Yace a zamanin Manzon Allah SAW ana amfani da Zakka da Wakafi ne wajen taimaka wa Marayu da masu karamin karfi dan rage musu radadin rayuwa.
Ya kuma ce burin wannan gidauniyar shi ne ba wai idan suka bai wa Marayu ko marasa galihu a wannan shekarar wata shekara ma su sake basu bane kamata ya yi ace wasu za a baiwa su kuma sun tsaya da kafarsu ta hanyar sana’o’i da suke yi da tallafin da aka basu.
Wasu Marayu da suka samu gudumawar sun jinjinawa kungiyoyin biyu akn yadda suka taimaka musu da kayan sallah.