Kamar yadda muka sha fada, a likitance ba ma katsalandan a addini kai-tsaye mu yanke hukunci har sai mun shawarci ko mun zauna mun tattauna da malaman addini.
Wato ke nan ko an fado jerin mutanen da mu a mahangarmu ba su kamata su yi azumi ba, dole sai da amincewar malamai, duk da cewa addini ya dauke wa wasu marasa lafiya azumin.
- Masu bai wa Gwamnatin Kano bashi su dakata —Abba Gida-Gida
- Tuna Baya: Yadda aka faro tafsiri cikin watan Ramadan
Ke nan akwai rashin lafiyar da ake ganin ba ta kai a dauke wa mutum azumi ba.
Don haka za a lissafo wadanda suke da larurar da a mahangar likitanci, ita kanta larurar ko don shan maganin larurar ba za su iya azumi ba, amma kuma kada a dauke shi a matsayin hukunci na karshe har sai an kara tambayar malaman addini a kusa ya amince.
Wadannan larurori su ne:
1. Mace mai juna biyu muna ganin azumi zai iya wahalar da ita ko dan da ke ciki
2. Mace mai shayarwa, muna ganin azumi zai iya wahalar da ita ko dan da take shayarwa
3. Mutum marar cikakken hankali
4. Mutum mai olsa ko gyambon ciki mai tsanani. Wanda bai yi tsanani ba ke nan zai iya gwada azumi
5. Masu ciwon suga nau’i na daya wadanda suke daukar allurai a-kai-a-kai.
Domin wasu alluran maganin ciwon suga aji na daya kan bukaci a yi su duk bayan ’yan awanni, kamar bayan awa hudu, wasu kuma shida.
To wadannan ka ga ba a jin za su iya azumi. Amma mai ciwon suga nau’i na biyu mai shan kwayoyi bayan awa 12 a rana zai iya.
Wanda kwayoyinsa sau uku ne a rana, wato duk bayan awa takwas, wani ana iya mayar da shi duk bayan awa 12 (kamar lokutan sahur da budebaki) idan sugansa na daidai, idan sugan ya rikice idan aka rage ka ga sai dai ya hakura.
6. Mai ciwon hanta wanda alamun ciwon suka fara bayyana, kamar shawara da kumburin ciki.
Mutumin da aka ce yana da ciwon hanta (kamar hepatitis) amma ciwon bai fara taba lafiyarsa ba, zai yi azuminsa.
7. Mai ciwon koda wanda alamun ciwon suka fara bayyana har ana masa wankin koda.
8. Mai ciwon zuciya wanda ke shan magungunan ciwon zuciya an fi so ya ajiye azumi saboda kada sinadaran jini na su sodium da potassium da chloride da magnesium da calcium wadanda zuciya take bukata sosai, su yi kasa
9. Mai Sikila ko ciwon ya tashi ko bai tashi ba, domin azumi zai iya ta da ciwon
10. Wanda aka ce yana da ciwon kansa kuma ya fara shan magani. Duk da cewa azumi zai iya taimaka wa kwayoyin kansa su motse, idan an fara magunguna wadanda lokacin shan su ko allurar su ya shiga lokutan azumi a iya bari.
Idan kuma za a iya canza lokutan su dace da lokutan cin abinci to shi ya fi.
11. Da ma duk wanda ciwonsa ya tashi ya yi tsanani ko shan magungunansa dole a sha awonnin kame baki.
12. Mai zazzabin maleriya a iya kwanakin da yake jinyar da shan maganin zazzabin
13. Mai zazzabin taifot a iya kwanakin da yake jinya da shan magungunan ciwon
14. Mai farfadiya wanda ke shan magunguna har a lokutan kame baki.
15. Masu ciwon yunwa. Ana kawo mutane asibitoci da dama a yanzu a kyamure da ciwon yunwa kawai a jikinsu ba wani alamun ciwo sai shi.
To irin wadannan ma a tsarin kulawa da su ana ba su ruwa da abinci ko madara duk bayan awa uku, yadda azumi ba zai yiwu ba sai sun warke.